✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin Audu da mahaifinsa

Barkanmu da Sallah Manyan Gobe Fatan alheri a gare ku.  A yau na kawo muku wani labari a kan bacin rai. Labarin na kunshe da…

Barkanmu da Sallah Manyan Gobe

Fatan alheri a gare ku.  A yau na kawo muku wani labari a kan bacin rai. Labarin na kunshe da yadda Manyan Gobe za su rika tunani kafin su bata ransu a kan abin da bai taka kara ya karya ba. A sha karatu lafiya.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi

Labarin Audu da mahaifinsa

Akwai wani yaro da ake kira Audu, ya kasance mai yawan fushi. Daga an yi masa magana sai ya bata rai. Rannan sai mahaifinsa ya ba shi kusoshi masu yawa. Ya ce masa idan ransa ya baci, sai ya buga daya daga cikin kusoshin a bango har sai ta nutse.
A ranar farko sai yaron ya buga kusoshi 37 a jikin bangon gini. Bayan sati biyu, sai ya fara kokarin rage yawan fushi saboda ba ya son kusoshin su yi yawa. Har dai ya ga cewa ya kamata ya koyi hakuri da a ce kullum shi ke nan buga kusa a jikin bango.
Wata rana  tun daga safiya har maraice bai buga ko kusa daya ba, domin ransa bai baci ba. Sai ya gaya wa mahaifinsa cewa yau bai buga kusa a bango ba, saboda ransa bai baci ba. Sai mahaifinsa ya ce, a duk ranar da ransa bai baci ba, ya sa hannunsa a jikin bango ya cire kusa daya.
Hakan aka rika yi har ya ce da mahaifinsa kusoshin jikin bangon sun kare. Kuma ya kasance mai hakuri yanzu.
Sai mahaifinsa ya rike shi a hannu ya kai shi wajen bangon. Ya ce da shi: “kayi kokari dana. Amma ka kalli ramukan da ka haka a jikin bangon nan”. Bangon ba zai taba canzawa ba. Haka kuma idan ka yi magana, to maganar na nan kamar tabo ne wanda ba zai taba canzawa ba.
Da fatan Manyan Gobe za su koyi darussan daga wannan labarin. Domin idan rai ya baci bai kamata hankali ya bata ba. Ya kamata a  zama masu hakuri da kuma sanin irin furucin da ya kamata a rika furtawa ko da rai ya bace.