✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labarin agogon manomi

Barka da warhaka Manyan Gobe Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo maku ‘labarin agogon manomi’. Wannan labarin zai koya wa Manyan…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo maku ‘labarin agogon manomi’. Wannan labarin zai koya wa Manyan Gobe yadda za su zama masu natsuwa a kodayaushe don cim ma burinsu.
A sha karatu lafiya.
Taku Gwaggo Amina Abdullahi

Labarin agogon manomi

An yi wani lokaci da wani manomi ya mallaki agogo mai matukar kyau. Rannan, yana cikin aiki a cikin rumbunsa, sai ya duba hannunsa don ya duba lokaci, sai bai ga agogon nasa ba. Haka ya sanya ya shiga neman agogon a rumbunsa. Ya duba duk inda yake tsammanin ganin agogon amma bai gan shi ba.
Daga nan ya yanke shawarar gaya wa yaran da ke wasa kusa da gonarsa. Ya ce su taimake shi su nemo masa agogon, kuma yana da wata babbar kyauta ga duk wanda ya samo masa agogon.
Yara suka shiga rumbu neman agogo don su samu kyauta daga manomi. Bayan sun yi minti talatin suna nema, sai suka fito daga rumbun babu wanda ya samu agogon. Sai manomi ya hakura.  Zai rufe rumbunsa ke nan, sai wani yaro daga cikin yaran ya ce da shi, a ba shi damar  sake shiga rumbun kila ya yi nasara.
Sai manomi ya ba shi dama. Bayan wadansu mintoci, sai yaron ya fito da agogo. Manomi ya yi mamakin yadda yaron ya samo agogo bayan ‘yan uwansa sun shiga kuma ba su gani ba. Sai  ya tambayi yaro yadda ya samo agogon? Sai yaro ya ce, bayan ya shiga rumbun, ya zauna shiru ne kuma ya natsu can sai ya fara jin karar agogon. A haka ya dinga bin karar har ya samo shi.
Manomi ya cika wa yaron alkawarin kyautar da ya yi niyyar ba duk wanda ya samo masa agogonsa.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labarin. Komai za ku yi yana da kyau mutum ya samu natsuwa don cim ma burinsa.