✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Labari da dumiduminsa: ’Yan bindiga sun yi garkuwa da Tsohon Minista a Nasarawa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarwa ta tabbatar da sace Tsohon Ministan Kwadago, Mista Hussaini Akwanga.   Akwanga ya yi aiki a Gwamnatin Olusegun Obasanjo amma…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarwa ta tabbatar da sace Tsohon Ministan Kwadago, Mista Hussaini Akwanga.
 
Akwanga ya yi aiki a Gwamnatin Olusegun Obasanjo amma aka sauke shi a ranar hudu ga watan Disamban shekarar 2003 sakamakon zargin badakalar Dala miliyan 214 na katin dan kasa.
 
Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Kennedy Idirisu wanda ya tabbatar da lamarin a garin Lafiya a ranar Laraba ya ce ’yan bindiga sun sace Akwanga a gonarsa da ke kan titin Wamba a garin Akwanga a ranar 22 ga watan Agusta.
 
Garin Akwanga yana daga kimanin kilomita 46 a Arewa da garin Lafiyar Jihar Nasarawa.
 
Idirisu ya ce suna samun rahoton aukuwar lamarin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Mista Abubakar Sadiq-Bello ya tayar da rundunar ’yan sanda karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ’yan sanda don su bi sawun wadan suka yi sace shi Tsohon Ministan.
 
Sai dai wata majiya da ke kusa da iyalan Tsohon Ministan ta tsaigunta wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya cewa wadanda suka yi garkuwa da shi sun tuntubi iyalansa inda suka nemi a basu makuden kudi  a matsayin kudin fansa.