✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyautar Nobel 2020 ta kubuce wa Trump

Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) ya lashe kyautar Nobel kan Wanzar da Zaman Lafiya ta 2020

Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) ya lashe kyautar Nobel kan Wanzar da Zaman Lafiya ta 2020, “saboda kokarinsa na yakar yunwa”.

Shugaban Amurka Donald Trump ya rasa kyautar da aka ayyana sunansa a cikin wadanda ganin za su samu ba.

An ayyana sunan Trump a jerin wadanda za a zabi gwarzon da ya cancanci kyautar ta bana ne saboda kokarinsa na daidaita al’amurara tsakanin kasar Isra’ila da makwabtanta na yankin Gabas ta Tsakiya.

Da farko an yi tunanin Trump na da gagarumar damar samun kyautar musamman a matsayinsa na Shugaban Amurka da gwamantinsa ba ta shiga yaki ba.

Yayi karbar kyautar a ranar Juma’a, WFP ta ce tana taimakon mutum miliyan 97 a kasashe 88 a duk shekara, kuma mutum daya a cikin kowane mutum tara a duniya ba ya samun isasshen abinci.

“Akwai bukata hadin gwiwar kasashe da hukummin duniya fiye da kowane lokaci”, inji Shugabar Kwamitin Kyautar Nobel kan Zaman Lafiya, Berit Reiss-Andersen.

WFP na kan gaba a kokarin da duniya ke yi na dakile yiwuwar amfani da yunkwa a matsayin makamin yaki ko rikici ko a yanayin COVID-19 wanda WFP din ta ce na ina ya matsalar yunwa a duniya ta ninku.

“Annobar coronaviru da taimaka wajen karuwar mutanen da ke fama da rashin isasshen abinci a duniya,” inji kwamitin na Nobel.