Babban jami’i a kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa don yaki da annobar coronavirus (PTF), Dokta Sani Aliyu, ya ce da zarar Gwamnatin Tarayya ta mallaki rigakafin cutar coronavirus za a yi wa al’ummar kasar nan allurar kyauta ba tare da sun biya ko sisi ba.
Dokta Aliyu ya fadi haka ne a ranar Laraba yayin wata hira da aka yi da shi a wani shiri na Sunrise Daily da gidan talabijin na Channels ya saba watsawa.
A cewarsa, gwamnati ta yi tanadin duk wani shiri kan yadda za a mallaki rigakafin cutar coronavirus tare da bayar da tabbacin cewa za a yi wa ’yan Najeriya allurar kyauta.
Ya ce, “a jiya ne Shugaban Kasa ya ba wa kwamitinmu ikon ci gaba da shirye-shiryen dangane da allurar rigakafin cutar coronavirus.”
“Shugaban Kasar ya kuma ba mu umarnin tabbatar an samar da allurar rigakafin a Najeriya.”
“Za mu kawo allurar rigakafin COVID-19 a Najeriya wanda a yanzu muna da tabbacin cewa za mu samu kashi 20 cikin 100 wanda za a yi wa kusan ’yan Najeriya miliyan 40 kyauta ba tare da sun biya komai ba,” inji Aliyu.
A yayin da muke fargabar cewa ’yan Najeriya za su juya wa rigakafin baya ta hanyar kin yarda a yi musu allurar, Aliyu ya ce suna kokarin ganin an wayar da kan mutane dangane da fa’idar samun rigakafin wannan cuta.
Ya ce, “Mun fara aiki tare da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da kuma Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Najeriya NPHCDA bisa la’akari da kwarewarta sosai wajen isar da alluran rigakafin a duk fadin kasar.”
“Saboda haka a yanzu babban kalubalen da za mu fuskanta shi ne yadda jama’a za su amince da ingancin rigakafin tare da juya wa allurar baya, don kalubalen da za mu fuskanta zai yai kamanceceniya da wanda fuskanta dangane da allurar rigakafin cutar shan inna.”