Fitaccen dan wasan Tennis, Novak Djokovic ya ce ya gwammaci a yi babu shi a duk wata gasar Tennis da za a yi nan gaba da a tilasta masa karbar rigakafin Coronavirus.
Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito Djokovic a wata ganawa da manema labarai yana cewa kada a danganta shi da kungiyar masu adawa da rigakafi, amma kuma ya goyi bayan a bai wa kowane mutum dama ta yin zabin karbar rigakafin ko sabanin haka.
- An tona asirin manyan ’yan sanda da NDLEA bayan Abba Kyari ya kwan a tsare
- An yi bikin cika shekaru 40 da fara yaye daliban aikin Jarida a Jami’ar Bayero
Da aka tambayi Djokovic ko zai iya hakura da shiga gasa kamar su Wimbledon da French Open saboda ra’ayinsa a kan rigakafi, sai ya kada baki ya ce, “kwarai, abubuwa ne da na yi niyyar sadaukarwa.”
A watan da ya gabata ne hukumomin Australia suka tisa keyar dan wasan da ya lashe manyan kofunan Grand Slam sau 20 gida, sakamakon sa-in-sa a game da tirjewarsa a kan rigakafi, duk da cewa ya karbi izinin likita na shiga kasar bayan da ya murmure daga cutar COVID-19 da ta kama shi.
Dan wasan wanda shine lamba daya a wasan Tennis ya ce ya kafe a kan haka ne saboda yanke shawara a kan abin da ya shafi jikinsa ya fi masa duk wata lambar yabo ko kudi da zai samu.