✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyauta da kyauta – yi don Allah ba ta rage dukiyar Musulmi (5)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya…

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya sanya yin kyauta da kyauta-yi cikin kyawawan dabi’un Musulmi.  Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma ya koyar da cewa kyauta da kyauta-yi ba ta rage dukiya; Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.  
Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, mun dakata a daidai inda muka ce a wannan makon za mu ga shi ma talaka ko yana da irin gudunmawar da yake iya bayarwa a karkashin tsarin na kyauta da kyauta-yi, to ga ci gaba:
Kowa yana da abin da zai iya bayarwa:
Shi Musulmi na gaskiya yana da dabi’a da hali na kyauta da kyauta-yi komai talaucinsa, kuma komai kankantar abin da ya bayar, ana lissafe shi a wannan matsayi. Kai, ya ma dai ishe shi a ce yana da shauki a cikin zuciyarsa da tausayin wadanda suka fi shi talauci, saboda yakan yi tunanin irin halin da suke ciki na rashi da babu. Duk yadda mutum ya kai ga talauci, to yau da gobe, sai ya samu wanda ya fi shi, shi ya sa hadisai da dama suke kwadaitar da mara shi ya bayar da komai kankantar abin da ya samu don Allah, gwargwadon karfi da iyawarsa, lamarin da zai sa ya ji shi ma ya bayar da tasa gudunmawar wajen taimakon wadansu. Shi bayar da dan kadan saboda Allah, idan mutum ya gan shi a Ranar Lahira zai yi ta mamakin yadda ya kai haka don girma, saboda Allah Yana kiwata masa shi ne a wajenSa, matukar dai abin da ya bayar din ya same shi ne ta hanyar halal.
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Duk wanda ya bayar da wata sadaka (ko kyauta) daidai da dabino daya na halal – domin Allah ba Ya karbar komai, sai mai tsarki (halal) – Allah Zai karba da hannunSa na dama, kuma Ya kiwata (Ya tattale) shi, kamar yadda dayanku yake kiwon maraki har ya zama bajimi – to Allah zai tattale shi har ya zama kamar girman tsauni a Ranar Lahira.”  Buhari da Muslim ne suka fitar da Hadisin.
Don ya kare mutane daga juya baya da kuma runtse idanunsu wajen bayarwa saboda Allah, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bukaci su bayar da sadaka komai kankantarta. In sun yi haka, za a samu kyautatawa da tausayi da rangwame da shaukin juna a cikin zukatansu da kuma tsakaninsu. Ya gargade su da su guje wa rowa da kankame dukiya, a hana ta zagayawa tsakanin jama’a mabambanta, lamarin da yake haifar da jafa’i da bala’i a tsakaninsu, a yayin da ya ce, “Ku kange kawunanku daga Wutar Jahannama ko da da bayar da kyautar (ko sadakar) rabin dabino ne.”  Buhari da Muslim ne suka fitar da Hadisin.
Allah Yana son Musulmi ya zama na kirki, mai amfani ga al’ummarsa, wanda kuma yake taimakawa a samar da kyakkyawa kuma kwakkwarar al’umma, wadda kodayaushe tana cikin alheri, ko Musulmin nan yana da wadata ko talaka ne shi. Wannan dalili ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya karsasa Musulmi ya kasance mai kyauta cikin kyauta-yi, gwargwadon iyawarsa da karfinsa, domin kowane irin aikin kwarai sadaka ne, inda ya ce, “Kowane Musulmi lallai ne ya bayar da sadaka.” Sai sahabbai suka ce, “Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), to in mutum ba zai iya haka ba fa?” Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Sai ya yi aiki da hannunsa ya samu abin da zai biya wa kansa bukata kuma ya bayar da sadakar!” Sai suka ce, “To, in ba zai iya haka ba fa?” Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Sai ya yi kokarin taimaka wa wanda yake cikin halin kaka-nika-yi (wato yake cikin tsananin matsi)!” Sai suka ce, “To, in ba zai iya haka ba fa?” Sai ya ce, “Sai ya yi wani abin kirki, ya nisanci mummuna, wannan zai kasance masa a matsayin sadaka.” Buhari ne ya fitar da Hadisin. Musulunci ya yalwata da’irar kyauta-yi ta yadda ta hade kowane gefe na rayuwar Musulmi! Wato in ka rasa wannan abu, to da wuya ka rasa wancan! Wanda yake cikin talauci, ko kadan kada ya karaya ya ce ba shi da abin da zai bayar ko ya yi, wanda zai samu martabar mai kyauta ko sadaka. Matukar dai ya mayar da hankali wajen yin abin da za a kalla a ce madalla, to yana matsayin kyauta ko sadaka, wadda za a ba shi gwaggwabar lada a Lahira, saboda maganar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya fada, wadda Imamul Buhari ya fitar cewa, “Kowane irin aikin kirki, sadaka ne.”
Musulunci ya bayar da tabbaci ga kowa cewa yana da gudunmawar da zai iya bayarwa wajen gina al’umma, ya karfafe ta, ya ciyar da ita gaba a harkokin yau da kullum ta yadda za ta kasance natsattsiya kuma tabbatacciya, wadda kowa zai yi alfahari da ita, alhali a karshe zai zama ya ci kyakkyawar riba.  Allah Ya sa mu dace!
Musulunci adalin addini ne mai rangwame ga matsayin kowane Musulmi. Bai dora wa kowa, sai abin da zai iya dauka. Bai cewa mutum ya bayar da dukiyarsa ma, sai dai daga abin da ya ci ya rage. Ba ya zargin mai kadan. Ya ma fi son kowa ya samu damar biya wa kansa bukatarsa, domin hannun sama ya fi hannun kasa (wato mai bayarwa ya fi mai karba matsayi)! Amma dai duk abin da ya yi saura, to (Musulunci) yana kwadaitarwar a yi kyauta da shi cikin kyauta-yi, saboda shi Musulmin kirki ba ya kankamewar abin hannunsa, ya yi rowa, domin ya koya daga addininsa na Musulunci cewa bayar da sadaka (da kyauta), abu ne mai kyau, alhali kankamewa da rowa, abu ne mummuna, kamar yadda Hadisin da Imam Muslim ya ruwaito ya fada cewa:
 “Ya kai dan Adam, idan ka bayar da abin da ya yi saura na dukiyarka, abu ne mai kyau gare ka; idan kuma ka ki bayarwa, ka rike abinka, to abu ne mara kyau gare ka. Babu zargi a kanka don ka rike abin da kake da bukatarsa. Ka fara bayar da kyautar ga wadanda suke makusantan bukata gare ka. Ka sani, hannun da ke sama ya fi hannun da ke kasa (wato ya fi kyau ka bayar da ka karba)!”
Musulmin kirki ba ya mantuwa wajen yin kyauta cikin kyauta-yi, musamman wajen bayarwa daga cikin abin da yake saura a hannunsa, bayan ya fitar da bukatun kansa da na iyalansa, ko da cikin irin ajiyar nan ta shirin ko-ta-kwana, ko kuma ajiyar da za a ce an kirga shi cikin mawadatan al’ummarsa.
Mu kwanan nan! Wassalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuh!