✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyauta da kyauta – yi don Allah ba ta rage dukiyar musulmi (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya…

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya sanya yin kyauta da kyauta-yi cikin kyawawan dabi’un Musulmi.  Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma ya koyar da cewa kyauta da kyauta-yi ba ta rage dukiya; Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.  
Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, mun kwana bayan mun koro bayani a karkashin kanun, “Allah Yana sane kuma ana musanyawa,” har muka kai daidai inda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Dukiyar da take taskance ita ce wadda aka bayar da ita saboda Allah.” A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ba da labarin wata tunkiya da aka yanka, aka yi ta rabon namanta, har sai lokacin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya tambayi ko me ya rage a cikinta, sai aka ce masa, “Karfata daya.” Sai ya ce, “An taskance komai na tunkiya, sai karfata daya kadai.” Imamu Tirmiziy ne ya ruwaito shi kuma ya ce Hadisi ne mai kyau, ingantacce.
Ga ci gaba:
A kan irin wannan garabasar ladar ce Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya rika karsasa Musulmi wajen yin kishi (gabda -kishin da ma ina da irin abin da wane ya samu, sai in yi kamarsa ko in fi shi) ga mutum biyu, inda ya ce, “Ba hasada (gabda-takara), sai dai a kan mutum biyu: (1) Mutumin da Allah Ya wadata shi da dukiya kuma Ya azurta shi da ciyar da ita a cikin abin da yake na gaskiya (wato saboda Allah); da kuma (2) Mutumin da Allah Ya ba shi ilimi da basira, yana aiki da shi kuma yana karantar da mutane.” Buhari da Muslim ne suka ruwaito Hadisin.
Dukiya dai ita ce kashin bayan sinadarin gudanar da al’amurran rayuwa a tsakanin al’umma, musamman idan aka dace da mai ita yana bayarwa don Allah kuma cikin abin da yake na gaskiya, don amfanin kowa da kowa; sai kuma wanda yake da ilimi da basira, kuma yana amfani da su wajen shiryar da al’umma wajen bin abin da yake daidai. Babu shakka idan aka samu haduwar wadannan mutum biyu a tsakanin al’umma, za a ga kyakkyawar al’umma, wadda sai dai a yi kamarta, amma ba a wuce ta da komai ba.
Saboda haka shi Musulmi na gaskiya yana bayar da dukiyarsa tare da sanin cewa za ta komo gare shi ta fuskar lada da kyautatuwar abin da ta baro tun farko. Wannan dalili ya sa yake bayar da dukiyar, alhalin ba ya jin ya wuce wuri ko kuma yana takura wa magadansa, balle ya hana musu samu daga gare ta, shi ya sa ba za a ga wata alamar rowa a cikin gudanarwarsa ba. Haka dai za a same shi mai tafiyar da al’amurransa a tsaka-tsakin yanayi domin yana lura da abin da shari’a ta gindaya masa a rayuwa.  
Hasali ma dai za a iske cewa abin da ya bayar na dukiyarsa saboda Allah ya fiye masa dadi a ransa, saboda ita ce tasa, a kan wadda ya taskance ta don magada, wadda da zarar ya mutu, za a raba ta a tsakaninsu. Wannan ne ma ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce wa sahabbai, “Wane ne ya fi son dukiyar (da zai bar wa) magadansa a kan dukiyarsa.” Sai suka ce, “Ya Manzon Allah, ba wanda yake son dukiyar magadansa a kan dukiyarsa.” Sai ya ce, “Dukiyar (mutum ta) gaskiya, ita ce wadda ya bayar (saboda Allah); amma dukiyar magadansa, ita ce wadda ya (mutu ya) bar musu.” Buhari ne ya ruwaito Hadisin.
Ita kyauta da kyauta-yi, daya ce daga cikin kyawawan dabi’un Musulunci da kuma Musulmi. Shi ya sa ma a yayin da wani mutum ya zo ya tambayi Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam), “Wane (aikin) Musulunci ne ya fi?” Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ciyar da mutane da yin sallama ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba.” Buhari da Muslim suka ruwaito Hadisin.
Ba a bude hannu duka:
Kada wajen zumudin samun lada mutum ya kwashe dukiyarsa gaba daya ya rabe ta, ya bar magadansa ba su da komai. Ba a bude hannu duka. Kowane irin al’amari na rayuwa, Musulunci ya tsara yadda ya kamata a gudanar da shi, sai dai mutum ya lura, kada ya kasa kuma kada ya wuce wuri. Kamar yadda bayar da dukiya saboda Allah yake da muhimmanci, haka ma tsare mutuncin magada, don kada a bari su koma mabarata a tsakanin jama’a.  Wannan kuwa ya dace da abin da ya gudana tsakanin sahabi Sa’adu dan Abu Wakkas da Annabi, lokacin da rashin lafiya ta tsananta gare shi, ya kai gargara.
Yayin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ziyarci Sa’ad (Allah Ya yarda da shi), don ya duba shi game da rashin lafiyarsa, sai ya ce masa, “Ya Manzon Allah, ina da dukiya mai yawa kuma ’ya’ya mata biyu kadai gare ni (da za su gaje ni), shin in bayar da kashi biyu cikin ukun dukiyata sadaka?” Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “A’a.” Sai ya ce, “To, in ba da rabi?” Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “A’a.” Sai ya ce, “To, kashi daya cikin uku fa?” Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ka bayar da kashi daya cikin ukun, amma dai shi ma yana da yawa!”
Daga nan ne sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya yi bayanin cewa, “Ka bar ’ya’yanka cikin wadata, ya fi ka bar su cikin talauci, su koma suna bara (ko rokon mutane). Kuma ka sani, ba abin da za ka bayar (kyauta ko sadaka), ba tare da an ba ka ladarsa ba, ko da loma ce da ka dauka ka sanya a cikin bakin matarka.” Buhari ne ya fitar da Hadisin.
Manzon Allah, Sarkin Kyauta!!
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), shi ne sarkin kyauta, madubi na gaskiya abin koyi dangane da kyauta da kyauta-yi.  Ba a taba samun wani nakasu daga wajen Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), dangane da kyauta ba, kuma bai taba hana mabukacin da ya roke shi wani abu ba.  In yana da abin da zai bayar, ba ya jinkiri; in kuma babu abin bayarwa a wannan lokacin, yakan hakurtar da mabukaci, ya saurari abin da za a ba shi.
Sahabi Jabir (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Ba a taba tambayar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), wani abu ya ce, ‘A’a’ ba.” Buhari da Muslim suka fitar da wannan Hadisi.
Allah Ya taimake mu wajen yin kyauta domin neman yardarSa, amin.  
Mu kwana nan, sai makon gobe, in Allah Ya kai mu. Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!