✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyandar Biri ta kara yaduwa a Najeriya — Kwararru

Ana daukar cutar ce daga dabbobi kuma ana yada ta a tsakanin mutane.

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce an samu karuwar yaduwar cutar kyandar biri a Najeriya.

Alkakuma sun nuna cewa a yanzu cutar ta bazu zuwa jihohi 26 ciki har da Abuja, babban birnin kasar.

Aminiya ta rawaito wani kwararren likitan fata, Dokta Muhammad Shakir Baloguna na cewa wannan lamari abin tsoro ne wanda yake bukatar a ba shi kulawar gaggawa da ta dace.

Dokta Baloguna ya shawarci al’ummar kasar da su rika kiyaye dukkan matakan kariye na dakile yaduwar cutar.

Mahukunta dai sun tabbatar da cewa ana daukar cutar ce daga dabbobi kuma ana yada ta a tsakanin mutane.

Tun daga farkon watan Janairun 2022 zuwa Augustan shekarar, an samu mutum 473 da ake zargi sun kamu da cutar, a inda aka tabbatar mutum 172 da suka kamu da ita a cikinsu.

Daga cikin jihohin da aka samu bullar cutar a Najeriya sun hada Legas (20), Ondo (16), Adamawa (13), Ribas (13), Delta (12), Bayelsa (12), Edo (9), Nasarawa (9), Anambra (7), Imo (7), Filato (6) da kuma Taraba (5).

Sauran sun hada da Kwara (5), Kano (5), Abiya (4), Kuros Riba (3), Borno (3), Oyo (3), Gombe (3), Katsina (3), Kogi (2), Ogun (2), Neja (1), Bauchi (1), Akwa Ibom (1), Ebonyi (1) da kuma Abuja (1).

Bayanan wanda aka samu daga Hukumar Kula da Cutuka Masu Yaduwa ta kasar, NCDC, sun nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar a 2022 kawo yanzu, ya fi na wanda aka samu a 2017 da 2018 da 2019 da 2020 da kuma na 2021.

Tun daga farkon shekarar 2022, kasashe da dama ke fuskantar bullar cutar ta kyandar biri, abin da ya sa shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Gebreyesus, ya ayyana dokar ta-baci a kanta a ranar 23 ga watan Yulin shekarar.