✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kyanda ta kashe mutum 685 a Zimbabwe

Akwai masu tsatssauran ra’ayi da ba su yarda da allurar rigakafin cutar ba.

Ya zuwa yanzu annobar cutar kyanda a Zimbabwe ta lakume rayukan mutane 685, fiye da sau hudu da aka samu rahoton bullar cutar a kusan makwanni biyu da suka gabata.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da yin allurar rigakafin cutar a fadin kasar.

Cikin wani sako da Ma’aikatar Lafiyar kasar ta fitar ranar Asabar a shafin Twitter, ta ce akwai mutane 6,034 da aka tabbatar sun harbu da cutar, wadanda suka hada da yara 4,266 da kuma mutum 685 da suka mutu.

Ma’aikatar ta ce an samu sabbin alkaluman mutum 191 daga cikin su 37 sun mutu ne a ranar 1 ga Satumba.

Bayanai sun ce da farko dai yara ‘yan tsakanin watanni shida zuwa shekaru 15 ne ke kamuwa sakamakon cutar.

Ministar Yada Labaran kasar, Monica Mutsvangwa ta ce cutar ta fi kamari musamman a kan wadanda suka fito daga bangaren masu tsatssauran ra’ayi da ba su yarda da allurar rigakafi ba.

RFI ya ruwaito gwamnatin na cewa, wasu kungiyoyin addinai ba su yarda da allurar rigakafin ba kuma sun dogara ne da addu’a.

Ko da yake har yanzu shugabannin coci-coci ba su mayar da martani ga ikirarin gwamnati na cewa imaninsu ne ke da alhakin yaduwar cutar kyandar ba.

Sai dai Mutsvangwa ta ce gwamnati na tuntubar shugabannin addini don samun tallafi da wayar da kan jama’a.