Hukumar Kwastam ta kama wani jami’in dan sanda na bogi da ya ce har ya kai mukamin Mataimakin Sufurtanda kan zargin fasa-kwaurin kayayyakin abinci na ketare.
Mukaddashin Kwanturola na Hukumar reshen Jihar Katsina, DC Dalha Wada Chedi ne ya bayyana hakan yayin holen wanda ake zargin ga manema labarai a hedikwatar Kwastam da ke birnin Dikko.
Ya ce wanda ake tuhumar ya shaida masu cewa shi dan sanda ne da ke karkashin sashen rundunar ’yan sandan masu sintiri a manyan hanyoyi a Jihar Kaduna.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, an kama jami’in na bogi mai suna Sirajo Jelani Abdulkadir da buhuna 25 na shinkafar waje, katan 2 na taliya da kuma katan 2 na makaroni.
Bayanai sun ce an kama mutumin ne a kan hanyar Katsina zuwa Kano a cikin wata mota kirar Toyota Sienna mai lambar LSD 315 FD, makare da kayan na fasa-kwauri.
Mukaddashin ya bayyana cewa, a binciken da suka gudanar sun samu wanda ake zargin dauke da katukan shaida ta bayyana-kanka wato ID. Card guda 4 mabambanta, rigar ’yansanda, ankwa da kuma gwangwanin hayaki mai sa hawaye.
DC Chedi ya ce tuni suka mika wa rundunar ’yan sandan Jihar Katsina mutumin domin ci gaba da bincika.
Dangane da irin nasarorin da Hukumar Kwastam ta samu daga watan Fabarairu zuwa Maris na wannan shekara, sun kama motoci dauke da buhunnan shinkafar waje har 432, taliya katan 309 tare da jarkokin man girki 68.
Sauran kayan da suka kama sun hada da buhunna Aya 400 da kuma katan 55 na makaroni wadanda kudinsu sun haura naira miliyan arba’in da biyu.