Daliban Najeriya da ke Sudan sun shiga halin rashin tabbas bayan da suka nemi jami’an Ofishin Jakadancin kasar a Sudan, suka rasa.
Hakan ta sa daliban da ke jira a kwaso su daga birnin Khartoum zuwa Masar yin da zanga-zanga, bayan da suka lura cewa jami’an ofishin jakadancin sun yi layar zana tare da iyalansu, sun bar su.
A garin haka ne suka yi arba da daya daga cikin jagororin dalibai da ke cikin masu hannu wajen tsara kwashe daliban, inda suka lakada masa duka, kafin a kwace shi daga hannunsu.
Wata maijiya ta ce jagoran daliban mai suna, Ibrahim Abdallah, yana daga cikin wadanda wadanda ke kai-komo tsakanin ofishin jakadancin da kuma kamfanonin jigilar da za su kwashe su daga Khartoum zuwa kasar Masar.
- Yau ’yan Najeriya 1,500 da suka makale a Sudan za su iso Abuja
- ’Yan Najeriya da suka je Umara sun makale saboda rikicin Sudan
Abdallah ya bayyana cewa tuni kudin kafin alkalamin da ofishin jakadancin ya ba wa kamfanin ya kare, kuma, “Zuwa yanzu da nake magana ba a [kara] sa ko sisi ba, tun da ba ko sisi, bas ba za su tashi ba,” duk da cewa motocin suna kasa na kwashe mutanen.
Ya bayyana cewa da za a biya motocin kudin, da kowa zai samu wucewa daga Khartoum a ranar Juma’a, “saboda bas 25 ne; kowa zai wuce, amma saboda [ofishin jakadanci] ba su ba da kudi ba, mai bas ya ce ba za a hau masa mota ba.
“…Gwamnatin Najeriya ce ba ta biya kudi ba; kudin da ake cewa an biya defosit ne, Dala dubu 250,” kuma an riga an gama da su.
Wannan sabuwar dambarwa ta kunno kai ne a yayin da wa’adin tsagaita wuta na kwana uku da bangarorin da ke yaki da juna a Sudan ke karewa a ranar Alhamis da dare.
Aminiya ta ruwaito cewa ofishin jakadancin a wata wasika ya bayyana cewa da wuya ci gaba da kwaso ’yan Najeriya da ke Sudan ya yiwu, saboda rikicin kudin hayar motocin kamfanin da suka dauka domin aikin.
Aminiya ta ruwaito cewa motocin farko da suka kwashe daliban sun yi watsi da su a tsakiyar sahara saboda rashin cika musu kudin aikin.
Ofishin ya bayyana cewa duk da cewa an kamfanin ya yi alkawarin ba su motoci 20 a kullum, amma takadamar kudin ta sa ya janye cikon motoci bakwai da ya bayar a ranar Laraba, wanda bisa alama, sun bayar da motocin iya kudin da aka biya su ne kawai.
Sai dai daga baya Hukumar Kula da ’yan Najeriya Mazauna Ketare ta ce an sasanta, motocoin za su karasa da daliban.
Daga bisani ofishin jakadanci ya nuna cewa bisa alama, kamfanin ya karashe wancan aikin ne daga defosit din da aka ba shi sannan ya dakatar da aiki.
Zuwa lokacin ofishin ya ce ’yan Najeriya 637 ne aka kwashe daga Khartoum a cikin bas-bas guda 13 zuwa iyakar kasar Masar da ke Aswan.
Hukumar kula da ’yan Najeriya mazauna ketare dai ta ce a ranar Juma’a 28 ga watan Afrilun da muke ciki ake sa ran isowar mutum 1,500 daga cikin ’yan kasar da suka makale a Sudan za su iso Abuja.