✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwarata biyu

Wata mata ce ta shirya dawani kwarto zai zo gidanta saboda mijinta ya yi tafiya, kafin kwarton ya zo sai ta sake shiryawa da kwarto…

Wata mata ce ta shirya dawani kwarto zai zo gidanta saboda mijinta ya yi tafiya, kafin kwarton ya zo sai ta sake shiryawa da kwarto na biyu shi ma ya zo. Lokacin da kwarto na farko ya zo sai suka zauna suna hira, sai kwarto na biyu ya zo ya yi sallama. Ta dauka mijinta ne ya dawo, sai ta ce kwarto na farko ya shiga kasan gado. Suna hira da shi sai mijinta ya dawo, sai ta ce masa: “Shiga kasan gado, dan uwanka yana ciki.” Da ya shiga sai ya sami kwarto na farko. Da mijin ya shigo sai suka zauna da matarsa a kan gadon suna hira, ashe a karkashin gadon akwai kaza tana kwanci, sai kazar ta tsakuri daya daga cikinsu, sai ya ce wa dayan: “Abokina, miciji sara yake ko cizo?” Sai ya ce masa sara yake, sai ya ce: “To kuwa ya saran.” Sai suka mike da gadon suka gudu.
Daga Sani Jimbo Kumbotso Kano 07035974135