✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwararrun ’yan wasa 10 za su fafata  a gasar kwallon tenis na Hukumar NCC

Gasar kwallon tenis na kusa da karshe na Hukumar NCC na shekarar 2018  wanda aka shirya shi a filin wasan na Enugu da filin wasa…

Gasar kwallon tenis na kusa da karshe na Hukumar NCC na shekarar 2018  wanda aka shirya shi a filin wasan na Enugu da filin wasa na kwallon tenis na kasa na Abuja zai nuna ‘yan wasa da tsoffin ‘yan wasa na kasa, wanda masu fashin bakin wasan tenis suka bayyana shi da abin tarihi.

Bayan fafatawar da aka yi zuwa wasan karshe tawagar ‘yan wasan Offikwu na Kaduna wanda suke da tsoffin ‘yan wasa da suka hada da Christie Agugbom da Silbesta Emmanuel da Henry Atseye da Shehu Lawal suka jagoranci tawagarsu ‘yan wasan Goshen na Ilorin a wasan na kusa da karshe wanda aka gudanar a Abuja a ranar 1 da ranar 2 ga watan Disemba.

‘Yan wasan Goshen za su sanya tsohuwar ‘yar wasa lamba daya Blessing Samuel wacce maza uku za su goya mata baya da Emmanuel Sunday da Uche Oparaoji da kuma Paul Emmanuel.

Daya daga cikin wasan na kusa da karshe wanda za a gudanar a Enugu a ranar 28 da ranar 29 ga watan Nuwamba zai nuna sabbin ‘yan wasan na kamfanin Leadway Assurance na Legas da tawagar Tech Bibe na Jos.

Tawagar ‘ya wasan tenins na Legas ta kunshi Babalola Abdulmumin da Clifford Enosoregbe da fitacciyar matar nan Sarah Adegoke da Albert wanda ya yi fice shi ma yana cikin tawagar. Abdulmumin da ‘yan tawagarsa ta Team Tech za su kara da bangaren maza wadanda suka hada da Joseph Imeh tsohon gwarzo da Thomas Out da kuma matashiyar nan mai suna Aanu Aiyegbusi.

Wadanda suka haye zuwa matakin na kusa da karshe za su samu miliyan biyu sannan wadanda suka yi nasarar za su sami miliyan bakwai sai wadanda suka yi kunnen doki za su sami miliyan biyar.