✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Kwararrun likitocin kwakwalwa dubu 10 ke aiki a kasashen waje’

Farfesa Lateef Sheikh Taiwo ya ce Gwamnatin Najeriya ba ta daukar likitocin bangaren da muhimmanci

Kwararren likitan kwakwalwar nan, Farfesa Lateef Sheikh Taiwo ya ce Gwamnatin Najeriya ba ta daukar likitocin bangaren da muhimmanci.

Farfesa Lateef Taiwo ya baygana haka ne a yayin zantawarsa da Aminiya a ofishinsa da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kan yadda suke samun kansu a yanayin aiki.

Ya ce rashin kulawar da gwamnati ke yi wa bangaren likitocin masu tabin kwakwalwa ya sa kwararru fiye da dubu 10 suka koma kasashen Amurka da Turai yayin da likitoci 300 ke kacal aiki a Najeriya.

Farfesa Lateef Sheikh ya ce babban abin takaicin shi ne yadda dukkan daliban da suka koyar da zarar sun kammala karatunsu wadannan manyan kasashen sai su ba su takardar zama a kasarsu ba tare da bata lokaci ba.

Ya ce rashin kyatatuwar aiki da rashin albashin da ya kamata da kuma rashin kayan aiki irin na zamani sannan ga babbar matsalar rashin tsaro da ya addabi Arewacin Najeriya suna cikin matsalolin da suke fuskanta.

Ya ce, kwararru a fannin sun yi karanci sosai a Najeriya saboda haka ya bukaci gwamnati ta waiwayi sashin don kai masa daukin gaggawa.