✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwaso ya yi belin ’yan Arewa 40 da ke tsare a Legas

A farkon makon nan ne Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya damka wa masarautar Agege matasa 40 cikin 71 da ya karbi belinsu a kan kuɗi…

 Sanata Kwankwaso a Legas, yayin miqa matasan da ya yi beli ga Sarkin Hausawan LegasA farkon makon nan ne Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya damka wa masarautar Agege matasa 40 cikin 71 da ya karbi belinsu a kan kuɗi Naira dubu 65 kowannensu kana ya ba su kyautar Naira dubu 20 kowannensu, a matsayin kudin mota, su je gida su huta bayan sun shafe fiye da kwanaki ɗari a tsare.
Sanatan mai wakiltar Kano ta tsakiya ya bayyana rashin jin daɗinsa bisa kamen da aka yi wa matasan ’yan Arewa, aka daure su na tsawon wattani uku cikin ukuba da yunwa, abin da ya sanya mutum biyar suka mutu a tsare. “Da ’yan Kudu ne aka tsare a Arewa to da ’yan uwansu ba za su yi gum da bakinsu ba, z aka ga suna ta yayatawa a kafafen watsa labarai, za kuma su dauki duk matakin da za a bi don ganin an sako ’yan uwansu. Amma mu a Arewa abin ba haka ba ne kuma ba abin da ya janyo mana haka illh jahilci. Don haka ina kira ga iyaye da su ba ilimin ’ya’yansu muhinmmanci, su sani cewa ba duk abin da suka samu za su badda shi a shan taushe da dage-dage da nama ba, a’a, ilimin ’ya’yansu shi ne ya fi muhinmmanci.” Inji Sanata Kwankwaso.
Ya shaida cewa mutanen Arewa ba za su ci gaba da zura ido ana cin fuskarsu ba, domin su ma da amfaninsu. Ya ce yunƙurin da Gwamnatin Legas ta yi a baya na sauya wa kasuwar mil 12, ba ya bisa ƙa’ida domin su suka raya wajen na kusan shekaru 40 a lokacin da yake ƙungurmin daji. Don haka a zo a rana tsaka a ce za a tashe su a sake maida su wani dajin ba abu ne mai yiwuwa ba, domin kamar yadda ’yan Arewa suke zuwa Kudu haka zalika ’yan Kudun ma na zuwa Arewa domin yin kasuwanci. Don haka dole ne a fahimci juna domin a zauna lafiya.
Matasan da aka ba da belinsu, wadanda aka yi masu shigar fararen kaya da jar hula, sun fito ne daga jihohi daban-daban na Arewacin ƙasar nan. Ya kuma umarce su da su je gida su huta, su nemi sana’a a can da tallafin da ya ba su. In kuma sun fi gane wa sana’arsu ta Legas, to su dawo su ci gaba ba tare da wata fargaba ba, domin suna da ’yancin zuwa ko’ina ne a cikin ƙasar nan domin biɗar arziki. Ya bukace su da su zamo masu bin doka da oda, ya kuma shaida masu cewa duk sadda aka neme su a kotu, to su hanzarta zuwa.
Sarkin Hausawan Agege, wanda ya karbi bakuncin Sanata Kwankwaso a fadarsa, ya yaba masa bisa kishin da ya nuna wajen ceton rayuwar matasan da aka tsare. Ya kuma yi masa addu’ar samun nasara a duk abin da ya sanya a gaba.