✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rokon Kwankwaso ga ’yan Arewa kan zaben Edo

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya nemi al’ummar Musulmi da ke Jihar Edo, da su tabbatar da nasarar Gwamna Godwin Obaseki yayin…

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya nemi al’ummar Musulmi da ke Jihar Edo, da su tabbatar da nasarar Gwamna Godwin Obaseki yayin zaben jihar da za a gudanar a karshen wannan mako.

Kwankwaso ya yi kiran ne a ranar Asabar 12, ga watan Satumba, yayin kaddamar da sansanin alhazai tare da Mista Obaseki a Benin, babban birnin jihar.

Ya nemi Musulmi a jihar da su fito kwansu da kwarkwata a ranar 19 ga Satumba, su zabi jam’iyyar PDP da hakan zai tabbatar da nasarar Gwamna Obaseki da mataimakinsa, Kwamared Philip Shu’aibu.

Tsohon Sanatan Shiyyar Kano ta Tsakiya ya yaba da kwazon gwamnan wajen kawo ci gaba a dukkan bangarori jihar, yana mai cewa bajintar da Obasaki ya yi a wa’adin farko za ta sa a sake zabensa a karo na biyu.

“Ina godiya ga mutanen Edo da Musulmai a jihar dangane da hadin kai da suka bayar wajen cimma nasarar kawo ci gaba a jihar.

“Wannan shi ne lokacin da dukkannin masu katin zabe kuma wadanda suka cancanci yin zabe, da mu fito baki daya don tabbatar da mun jefa wa jam’iyyar PDP kuri’unmu.”

“Ina kuma kira gare ku musamman wadanda suka fito daga yankin Arewacin kasar nan da su tabbatar sun jefa wa PDP kuri’unsu a ranar 19 ga watan Satumban 2020.

“Ina rokon ku zabi PDP, ku kare kuri’unku kuma ku tabbatar Obaseki da mataimakinsa, Shu’aibu sun ci zabe mai zuwa a jihar.

“Ina kuma kiran ku da ku tabbatar kun yi addu’ar samun zaman lafiya a jihar”, inji Kwankwaso.