Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP na daga cikin mtuanen da suka jefa ’yan Najeriya miliyan 100 a kangin talauci, inji Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Leba.
Peter Obi yayi wa Kwankwaso wankin babban bargo ne kan kalamansa cewa an jima da barin al’ummar Ibo da ma yankin Kudu maso Gabashin Najeriya nisa a baya a siyasar Najeriya.
- Buhari zai tafi Senegal jim kadan bayan Harin Kuje
- Babu dan Boko Haram ko daya da ya rage bayan harin Kuje —Ministan Tsaro
Kwankwaso ya yi furucin ne bayan Peter Obi ya yi watsi da tayin da ya yi masa na zame mishi abokin takararsa a zaben 2023.
A tattaunawarsa da wani gidan talabijin a Najeriya, Peter Obi, ya ce irin kalaman na Kwankwason ne silar samun yara miliyan 18 marasa zuwa makaranta da kuma samun rashin aiki a tsakanin kaso 55 cikin 1oo na ’yan Najeriya.
“Irin kalaman nan na uban gidana Kwankwaso ne suka jefa kasarmu matsaloli da rashin tsaro, saboda rashin duba cancanta da kuma sanya addini da banganranci a siyasa.
“Sanin kowa ne a kasar nan yanzu, ba ma iya zuwa Kaduna daga Abuja a mota, ko a jirgin kasa ko a na sama.
“To za ka ce saboda wanda ya fito daga yankin Kudu maso Gabas ne yake shugabancin kasar ne haka ya faru?
“Haka kuma ba za ka iya tafiya daga Abuja zuwa Minna ba a mota, shi ma duk don wanda ya fito daga yankinmu ne ke shugabanci aka samu hakan?” In ji shi.
“Jiya muka samu labarin yadda ’yan bindiga suka harbe ’rakiyar shugaban kasa a Katsina.
“Dubi yadda kayan abinci ke tsada, babu wutar lantarki, sannan al’ummar yankin da Kwankwason da shugaban kasar suka fito, fama suke da tarin matsaloli duk da su ke jagorantar kasar,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Babbar matsalar da ake samu a Najeriya shi ne zabar shugabannin da ba za su iya jagorantar kasarba; Ni a tsaye nake wajen jajircewa don magance matsalolin Najeriya, duk da suna da tarin yawa”.
A baya dai an sha rade-radin hadewa tsakanin Kwankwason da Peter Obi, inda magoya bayansu ke hasashen yadda farin jinisu a wurin matasa zai sa Jam’iyar NNPP ta Kwankwaso ta samu nasara a zaben 2023.
Sai dai kuma takaddama kan wanda zai tsaya a matsayin shugaban kasa tsakanin su biyun ya sanya hakan bai yiwu ba.
Rahotanni dai sun nuna tsayawa kan bakar kowanne daga cikinsu cewa shi zai jagoranci kasar ne ya sanya suka yi watsi da hadakar, suka ci gaba da zama a jam’iyyunsu.
A karshen makon jiya ne Kwankwason ya fito ya ce maganar yin hadakar ta watse.