Gwamnatin Tarayya ta ce kwanan nan Najeriya za ta fara kera jiragen yaki marasa matuka.
Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkira, Dokta Ogbonnaya Onu ne ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da kwamitin aiwatar da yarjejeniya tsakanin gwamnati da kamfanin Wise Guide Technology a Abuja ranar Litinin.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 18 suna sallah a masallaci a Neja
- Juyin mulki: Sojojin Sudan sun hallaka masu zanga-zanga 2, su raunata 80
A cewar ministan, yarjejeniyar ta tanadi ayyukan bincike ne da kuma bunkasa fasahar sarrafa jiragen yakin da basu da matuka.
Dokta Ogbonnaya ya ce matukar Najeriya na son karanta ya kai tsaiko a zamanance, dole sai ta fara kera dukkan kayayyakin da take bukata a cikin gida.
Hakan, a cewarsa zai taimaka matuka wajen samar da ayyukan yi, bunkasa tattalin arziki da kuma rage matsanancin talauci.
Ya ce Najeriya za ta ci gaba da bincke har sai ta fara sarrafa kayayyakin amfaninta, musamman a bangarorin noma da tsaro da harkar man fetur da kuma iskar gas.
Daga nan sai ya yi kira ga kwamitin da ya yi aiki tukuru a cikin makonni biyun da aka debar masa wajen ganin hakar gwamnatin ta kai ga cimma ruwa.