✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwana hudu a jere coronavirus na raguwa a Najeriya

Alkaluman masu kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya na ci gaba da raguwa a cikin kwanaki hudu a jere. Hakan na zuwa ne yayin da…

Alkaluman masu kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya na ci gaba da raguwa a cikin kwanaki hudu a jere.

Hakan na zuwa ne yayin da masu cutar suka haura 16,000 a jihohi 35 ba babban birnin kasar , Abuja.

Daga Alhamis 11 zuwa Lahadi 14 ga watan Yuni sabbin masu harbuwa da cutar sun yi ta raguwa daga 681 zuwa 403.
A dan tsakanin ne kuma wadanda suka warke suka kai mutum 5,220 bayan an sallami karin wasu 726 da suka warke daga cutar a Najeriya inda mutum 16,085 suka taba harbuwa ita.

Sai dai kuma cutar ta kashe mutum 420 a Najeriya, wadanda 33 daga cikinsu sun rasu ne a kwanaki hudun da suka wuce.

Alkaluman ranar 15 ga watan Yuni sun nuna mutum 403 ne suka kamu da cutar a ranar daga jihohi 20.

Yanzu mutum 10,445 ne suka rage a Najeriya dauke da cutar coronavirus wadda aka riga aka yi wa mutum 92,924 gwajinta.

Bayanai daga hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya sun ce jihar Kuros Riba ce kadai cutar ba ta bulla ba kasar.