✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwana 3 kafin Zabe: Majalisa ta amince a bai wa Kogi Naira Biliyan 10.69

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince a bai wa Gwamnatin jihar Kogi Naira Biliyan 10.069 don kaddamar da wasu ayyuka a jihar daga Gwamnatin Tarayya. Sai…

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince a bai wa Gwamnatin jihar Kogi Naira Biliyan 10.069 don kaddamar da wasu ayyuka a jihar daga Gwamnatin Tarayya. Sai dai ‘Yan Majalisar Dattawan jam’iyyar adawa ta PDP sun yi korafin cewa, kudin ya yi yawa kasancewar kwana uku ya rage don yin zaben Gwamna Jihar.

Shugaban marasa rinjaye na Majalisa Enyinnaya Abaribe, (Dan jam’iyyar PDP, daga jihar Abiya ta Kudu) ya bukaci a dakatar da bayar da kudin zuwa nan da mako daya saboda kar gwamnatin jihar ta karkatar da kudin wajen yin zaben Gwamnan jihar.