✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin Wa’azi: An ja daga tsakanin gwamnati da malamai

Malaman addini na yin kashedi ga El-Rufai da kwamitin kula da wa'azi a Jihar Kaduna.

A ranar Asabar da ta gabata ce, Gwamnatin Jihar Kaduna ta kaddamar da kwamitin da zai rika kula tare da bayar da izinin yin wa’azi a jihar ga mabiya addinan Musulunci da Kirista.

A cewar gwamnati, an samar da dokar ce domin kawo karshen fadace-fadace da sunan addini musamman a tsakanin Musulmi da Kirista a jihar.

Abin da ya sa muka samar da dokar —El-Rufa’i

A jawabin Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai wanda shi ne ya kaddamar da kwamitin wanda ya kunshi malamai da masu rike da sarauta da jami’an tsaro, ya ce aikinsu shi ne kula da yadda ake wa’azi a jihar.

A cewarsa, a lokuta da dama an samu tashin hankali a Jihar Kaduna wanda a cewarsa yawanci saboda irin maganganu da kalaman da malaman addinai suke yi ne da sunan wa’azi ke rura su.

Gwamnan ya ce kamata ya yi addini ya hada kan mutane su san cewa dukkansu halittun Allah ne su fahimci junansu sannan su san cewa Allah daya ne duk da kowa na bauta miShi ne ta yadda ya fahimta.

Ya ce bambancin addini bai kamata ya kawo kashe-kashe ba ko tashin hankali cikin al’umma, wanda a cewarsa hakan ya sa tsohon Gwamnan Soji na Jihar, marigayi Iya Mashal Usman Mu’azu a 1984 ya yi dokar da ke bukatar samun manyan malamai da sarakuna da jami’an tsaro su rika duba mutane kafin a ba su damar yin wa’azi ko a masallaci ko a coci.

Gwamna El-Rufa’i ya ce gwamnatin Kanar Hamid Ali (mai ritaya) ta kara gyara dokar ta kara mata karfi ta sanya tara da zuwa kurkuku idan mutum ya saba mata.

“Da muka zo a shekarar 2016 muka tura wa Majalisar Dokoki don ta duba a sa dimokuradiyya a ciki sannan a dubi abubuwan da suka faru a jihar a ga me za a iya gyarawa domin mu hana shugabannin addini yin maganganu da za su kawo tashin hankali a jihar.

“Majalisar Dokokin Jihar ta gyara dokar kuma ta yi abin da ake bukata a dokar, wanda shi ne a samu majalisar malamai da jami’an tsaro da za su rika duba duk mutumin da zai hau mumbari yin wa’azi a Jihar Kaduna, sai wannan kwamiti ya ba shi dama zai iya yi in kuma ka yi ba tare da wannan ba, akwai tara akwai zuwa kurkuku idan kotu ta same ka da laifi,” inji shi.

Sai dai wanan matsayi na gwamnati ya janyo ce-ce-ku-ce a jihar inda malaman addinan biyu suka soki dokar.

Mambobin kwamitin sun hada da Alhaji Mannir Jafaru Madakin Zazzau, wanda shi ne Shugaban Kwamitin da Comfort Bankoji da Sheikh Kabir Kasim da Iliya Duniya da Sheikh Is’haq Yunus sai Rabaran Simon Haruna.

Sauran su ne Kwamishinan ’Yan sandan Jihar da Daraktan Hukumar DSS sai Shugaban Hukumar Kula da Addinai sai Kwamnadan ’Yan Sintiri na Jihar da Babban Sakataren Ma’aikatar Tsaro da Al’amuran Cikin Gida.

Gwamnati ba ta da hurumin ba wa mai wa’azi lasisi – Sheikh Maraya

Da yake amsa tambayoyin wakilin Aminiya kan batun, Sheikh Halliru Maraya, wanda daya ne daga cikin manyan malaman addininin Musulunci a jihar, ya ce akwai bukatar ’yan kwamitin da aka kafa su sani ba su da hurumin tantancewa ko ba wa masu wa’azi lasisi domin Tsarin Mulkin Najeriya, Sashe na 38 Karamin Sashe na Daya ya bai wa duk dan Najeriya damar yin addinin da ya ga dama ya kuma canja addini kuma ya yada addininsa wato ya yi wa’azi shi kadai ko tare da sauran ’yan uwa ’yan kasa.

“Bayan haka Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yanke hukunci a watan Yulin shekarar 2019 wadda Mai shari’a Hajaratu Gwadah ta jagoranta cewa Gwamnatin Jihar ba ta da hurumin tantancewa ko ba masu wa’azi lasisi saboda haka nake kira ga wannan majalisa ta lura da wannan al’amari kada ta shiga abin da ba huruminta ba ne.

“Shawarar da zan ba su ita ce dama an kira su ne a matsayin kwamiti na ba da shawara, don haka duk mai wa’azi da suka gani yana wa’azin da bai kamata ba shi ne su kira shi su ba shi shawara in ma hukunci ne sai su ba gwamnati shawara ta dauka.

“Amma babban abin da ke damun masu wa’azi shi ne a ce wai gwamnati ce za ta tantance su sannan ta ba su lasisin sannan bayan shekara kuma sai a sabunta lasisin.

“Wannan shi ne dama ya dami masu wa’azin Musuluncin da na Kirista kuma tuni Babbar Kotu ta yi hukunci cewa gwamnatin jihar ba ta da hurumin haka.

“Iyaka ita hukuma ta sa ido ne ta kuma bude kunnuwanta ta ga cewa duk mai wa’azi da ke yin na tashin hankali ko yake wa’azin batanci sai su yi masa nasiha ko su ba gwamnati shawarar cewa mai wa’azi kaza ya kamata a hukunta shi a gaban sha’ria, wannan shi ne kiranmu ga wannan kwamiti da aka kafa.

“Kuma su sani cewa ba huruminsu ba ne su ba da lasisi sannan ba huruminsu ba ne tantance masu wa’azi domin tsarin mulkin ya rigaya ya ba duk wani dan Najeriya damar yin wa’azi.

“Ita kanta gwamnatin an ce ba ta da hurumi ballantana abin da ta kafa.

“Muna yi wa majalisa fatar alheri, amma kowa ya je ya yi wa’azi iyaka dai wanda ya saba ka’ida a hukunta shi wannan shi ne abin da ya kamata,” inji shi.

Addini ba abin wasa ba ne – Fasto Buru

A nasa jawabin, Fasto Yohana Buru cewa ya yi yana kallon wannan mataki ne ta fuskoki biyu.

“Da farko dai dokar tana da kyau domin akwai baragurbin malamai a kowane bangare, ma’ana a cikin addinin Musulunci da kuma na Kirista, wadanda ba addini ko mabiya addini suke so ba, sun dai shiga yin wa’azi ne domin biyan bukatun kansu,” inji shi.

Ya ce ire-iren wadannan malaman addinai ana iya amfani da su domin cutar da addini a cikin Musulunci ko Kiristanci ko su kawo wasu irin akidu da suka saba koyarwar Alkur’ani da Baibul.

“Ma’ana ita ce dokar ta yi daidai a dauki mataki a kan irin wadannan malamai ko fastoci domin samun zaman lafiya.

“Saboda idan babu kyakkyawar fahimta da ilimi a tsakanin mabiya addinai dole a samu rigingimu da fitinu a cikin al’umma.

“Amma a gefe guda akwai mishkila idan ba a samu tattaunawa da dukkan bangarorin da abin zai shafa ba, wanda ba kuma za mu goyi bayan hakan ba.

“Matsalar, dole sai an saurari sauran bangarorin da ke cikin Kiristanci da na Musulunci domin jin ta bakin kowannensu da fahimtarsa a kan wannan dokar domin abin addini ba abin wasa ba ne.

“Kila akwai wani malami da wani dan kwamitin ba ya jituwa da shi ko wani ya je ya yi korafi a kansa kafin a ankara sai a ga an ce wai an same shi da laifi.

“Shawarata a nan ita ce sanya ido ba shi ne abin damuwa ba, amma yadda za a sanya idon shi ne abin lura.

“Ina ba su shawarar domin wani na da abin fadi amma saboda tsoron gwamnati ko wata kungiya sai ya yi shiru.

“Saboda haka su mayar da hankalinsu a kan abin da aka ce su yi ba tare da sun wuce gona da iri ba.

“Idan abu ya faru a Kiristanci ko Musulunci su bincika tukunna kafin su ba da shawarar yin hukunci don haka su yi taka-tsantsan domin kada wankin hula ya kai mu dare,” inji shi.