✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin matasan JIBWIS ya tallafa wa kurame da tufafi

Kwamitin wa’azin matasa na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah, reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, ya shirya wa kurame da…

Kwamitin wa’azin matasa na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah, reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, ya shirya wa kurame da nakasassu sama da 250 wa’azi  tare tallafa musu da kayayyakin tufafi da kudi, a babban masallacin Juma’a da ke garin Jos.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin wa’azin matasan reshen, Ustaz Muhammad Kabiru Cidawa ya bayyana cewa sun shirya taron ne ganin akwai bukatar  a tallafa wa nakasassun. “Don haka muka ware masu wannan  rana ta musamman, muka gabatar masu da wa’azi da  ba su tallafin tufafi na maza da mata tare da sabulu da takalma da kudi, alhali nakasassun sun kai su 250”.
Ustaz Kabiru ya ce baya ga wannan shiri na tallafa wa kurame da nakasassu, akwai ziyarar gidajen yari da asibitoci da tallafa wa dattawa marasa karfi da aka sanya a gaba.
Ya ce, in Allah Ya yarda, a watan Ramadan mai zuwa za su tallafa wa marayu da kayayyakin sawa a garin na Jos, musamman ganin akwai marayu da dama a cikinsa.
Ya yi kira ga al’ummar musulmi su riki ayyukan tallafa wa al’umma, musamman gajiyayyu da marasa karfi. Ya ce, “Muna da marayu a ko’ina, muna da marasa lafiya da suke kwance a asibitoci da gidaje da dattawa da suke neman tallafi, don haka mu tashi mu yi kokari mu tallafa wa irin wadannan mabukata”. Inji shi.
A wajen taron dai,  malaman da suka gabatar da wa’azi sun hada da shugaban makarantar Albayan, Malam Ibarahim Imam Shehu Gwandu, wanda ya yi nasiha kan jin tsoron Allah; da Limamain masallacin Juma’a na ’yan doya, Sheikh Aliyu Aliyu, wanda ya yi wa’azi kan dogaro da kai.