Kwamitin da gwamnatin jihar Legas ta kafa domin bincikar zargin cin zali da karya ka’idar aiki da wasu jami’an ‘yan sanda suka yi a jihar zai fara zamansa a ranar Litinin domin fara gudanar da bincike.
Tsawon makonni biyu kenan matasa suka shafe a fadin Najeriya suna gudanar da zanga-zangar dake neman a rushe sashen ‘yan sanda na SARS.
- Zalunci: An fitar da sunayen ’yan sandan da za a hukunta
- #ENDSARS: An zakulo ‘yan sanda 16 da za a hukunta
Zanga-zangar ta #EndSARS ta jawo rasa rayukan mutane da dama, ciki har da jami’an tsaro, mutanen gari da ma dukiyoyi na miliyoyin Nairori.
Matasan Najeriya sun yi kira ga gwamnatin Najeriya akan lallai sai an kawo karshen zaluncin ‘yan sanda, wanda gwamnati ta amince tare da rushe rudunar tsaron ta SARS a fadin kasa.
Sai dai daga bisani zanga-zangar ta rikide zuwa rikici a sassan kasar nan, inda wasu bata gari suka shiga aikata laifuka da suka hada da satar kayan mutane, fasa manyan shaguna, Bankuna, kayan mutanen gari dana gwamnati.
Jihar Legas ita ce, jiha ta farko da ta fara kafa kwamiti domin bincikar laifukan da ake zargin ‘yan sanda sun aikata.
Hakan ne ya sanya gwamnatin jihar wallafa sunayen wasu jami’an ‘yan sanda da ake zarginsu da aikata laifukan da suka shafi cin zarafi da karyar doka aiki a makon da ya gabata domin fara bincike akansu.