Cutar COVID-19 ta kama Kwamishinar Lafiya ta Jihar Kaduna, Amina Mohammed-Baloni.
Kwaminishinar ta sanar da hakan ne ta shafinta na Twitter a ranar Juma’a inda ta ce tuni ta fara killace kanta domin samun kulawa.
- Sai mun ga bayan ta’addanci a Najeriya a 2021 —Buhari
- Kotu ta yanke wa matashi hukuncin bulala a Kano
- ‘Dalilin da muka hada bikin shan rake’
“Bayan sanarwar da na samu cewa na kamu da cutar, na fara killace kaina yadda ya kamata.
“Ina fatar samun sauki cikin sauku da wuri, kuma ina rokon kowa ya bi matakan kare lafiya na COVID-19 da suka hada da sanya takunkumi a cikin jama’a; tsaftacce hannu a-kai-a-kai; da kuma guje wa shiga taron jama’a,” inji ta.