✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamishinan Legas ya ajiye mukaminsa saboda yawan rushewar gine-gine

Ajiye mukamin nasa na da nasaba da rushewar gine

Kwamishinan Tsara Birane na jihar Legas, Dokta Idris Salako, ya ajiye mukaminsa.

Kodayake ba a san ainihin makasudin ajiye mukamin nasa ba, amma ana hasashen hakan ba zai rasa nasaba da yawan rushewar gine-gine a jihar ba.

Bayan rushewar gini mai hawa 21 da ke kan titin Gerard a Ikoyi a watan Nuwamban bara wanda ya kashe mutum 41, ciki har da mamallakinsa, wasu gine-ginen da dama kuma sun sake rushewa.

Ko a sanyin safiyar Lahadi dai sai da wani gini mai hawa bakwai da ke kan titin Oba Idowu Oniru, ya rushe, inda ya kashe mutum hudu, ya kuma kuma jikkata wasu hudun.

Wani masani, Victor Onyenuga, ya zargi yawan rushewar gine-ginen da kasa a gwiwar da gwamnatin jihar ta yi wajen aiwatar da shawarwarin da aka ba ta a baya.

Tuni dai Gwamnan jihar ta Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya amince da ajiye mukamin Kwamishinan.

A cewar Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Gbenga Omotosho, ya ce ajiye mukamin na da alaka da sauye-sauyen da ake kokarin yi a ma’aikatar.