✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwamishina ta yi murabus bayan an tube wa mahaifinta rawani

Sa'adatu Bello Kirifi ta yi murabus washegarin sauke mahaifinta daga sarautar Wazirin Bauchi

Kwamishinar Bunkasa Kungiyoyi, Kananan da Matsakaitan Sana’o’i ta Jihar Bauchi, Sa’adatu Bello Kirifi, ta ajiye mukaminta, bayan an sauke mahaifinta daga sarauta.

Sa’adatu Bello Kirifi ta yi murabus ne kasa da awa 24 bayan an tube wa mahaifin nata, Alhaji  Muhammadu Bello Kirfi, rawaminsa na Wazirin Bauchi tare da sallamar sa daga Majalisar Masarauar a ranar Talata.

A takardar ajiye aikin da ta aike wa Gwamna Bala Mohammed ranar Laraba, Honorabul Sa’adatu ta ce, “Ina mika takardata ta yin murabus daga Majalisar Zartarwa da kuma kujerar Kwamishinar Bunkasa Kungiyoyi, Kanana da Matsakaitan Sana’o’i ta Jihar Bauchi, ba tare da bata lokaci ba.

“Ina godiya ga Gwamna da ya ba ni damar yi wa Jihar Bauchi aiki a gwamnatinka.

%d bloggers like this: