✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kwallon dawaki ba na masu kudi ba ne kawai – Mamman Gashash

Aminiya ta samu tattaunawa da Hassan Mamman Gashash wanda shi ne Sakatren kungiyar wasan kwallon dawaki na kasa kuma shi ne Sakatren kungiyar kwallon dawaki…

Aminiya ta samu tattaunawa da Hassan Mamman Gashash wanda shi ne Sakatren kungiyar wasan kwallon dawaki na kasa kuma shi ne Sakatren kungiyar kwallon dawaki ta garin Jos kuma mataimakin shugaban masu sharhi kan kwallon dawaki na kasa. Gashash ya bayyana kalubalen da kwallon dawaki ke fuskanta da kuma nasarorin da suka samu. Ga yadda hirar ta kasance:

Abubakar Haruna, Daga Minna

Za ka bayyana dalilin da suka sanya kuka shirya wannan wasa a garin Minna?
Mun shirya wasan a garin Minna ne don sada zumunci kuma wasa ne da aka shirya a tsakanin kungiyoyi daban-daban kamar  su kungiyar kwallon dawaki ta Minna Bosso da kungiyar  Jos Malcomine da kungiyar kwallon dawaki ta Katsina da kungiyar kwallon dawaki ta garin Fatakwal da sauran kungiyoyi masu yawa.
Mene ne dalilin da ya sa kuka shirya wannan wasa?
Kamar yadda aka saba kungiyar  wasan kwallon dawaki takan shirya wadannan wasannin don sada zumunci kuma wasan ya samo asali ne tun lokacin Sarkin Katsina wanda ya taho da shi tun kimanin shekaru 100 kenan da suka gabata. Saboda shi wannan wasa an fara shi ne tun shekarar 1904 a wannan kasa. Babu abin da za mu ce wa Sarkin Katsina na wancen lokaci Sa Muhammadu Dikko da ya yi tunanin shirya shi wannan wasa na kwallon dawaki sai dai mu yi masa addu’a.
Me kake ganin shi ne babban kalubalen da kungiyarku ta harkokin kwallon dawaki take fuskanta?
Gaskiya muna fuskantar kalubale daban-daban musamman ma abinda ya shafi lamarin kudi. Muna fuskantar karancin kudi. Ba kamar yadda aka saba a shekarun baya ba inda ake kashe kudi masu yawa. Ka san shi kwallon dawaki abu ne da yake bukatar kudi mai yawa. To a yanzu gaskiya abin sai a hankali. Musamman idan ka yi la’akari da yadda wannan gwamnati ta rike kudi. Ka san shi kuma doki dole ne sai ka ba shi abinci ka dauki dawainiyar wanda zai kula da shi da kuma lura da lafiyarsa  da makamanatansu. Saboda haka da ma mukan hada gwiwa da gwamnatoci da kamfanoni masu zaman kansu don daukar nauyin wasan da za mu yi amma a yanzu gaskiya kusan kowa korafi yake yi cewa babu kudi.Kafin wannan kuma kalubalen tsaro shi ma ya taimaka kwarai da gaske wajen kawo mana cikas a harkokinmu. Ka san halin tarbabarewar tsaro musamman Arewacin Najeriya ta shiga a shekarun baya kafin zuwan wannan gwamnati. Amma muna yi wa Allah godiya da kawo saukin lamarin yanzu abubuwa sun fara komawa daidai kamar yada aka saba.
Mutane za su yi mamakin idan suka ji cewa kuna fuskantar kalubalen kudi don shi wannan wasa na masu hannu da shuni ne?
E gaskiya ne amma abin da mutane yakamata su gane shi ne shi wannan wasa ba wai kawai na attajirai ne kawai ba saboda haka su kansu attajiran suna yin iya bakin kokarinsu wajen ganin sun tallafawa wasan komai ya tafi daidai kamar yadda aka saba. Ka san shi ajiye doki kamar ka ajiye mata hudu ne. Ka ga kamar Muhammadu Babanagida shi kadai yana daukar nauyin kungiyoyi masu yawa kuma akwai irinsa masu yawa da ke daukar dawainiyar kungiyoyi masu yawa.Haka shi ma kanin gwamnan Jihar Neja shi ma yana daukar dawainiyar kungiyoyi masu yawa.
Kana nufin su ma kansu attajiran sun ji jiki kenana?
Gskiya kowa a yanzu yana taka-tsantsan don kowa a yanzu ya ji a jikinsa saboda matakan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake dauka wajen ganin tattalin arzikin kasa ya gyaru. Saboda haka shi ya sa ka ga kowa yana bi a sannu a hankali tare da lura da abin da ke kai kawo. A da idan mutum yana kashe Naira 100 zai dawo yana kashe Naira ashirin ya koma daki ya zauna ya saurari dokokin da gwamnati za ta bullo da su.
Wadanne nasarori za ka iya bayyanawa kun samun kawo yanzu?
Gaskiya mun samu nasarori da yawa wadanda suka hada da shirya wasanni masu yawa kuma mu ba kamar sauran wasanni ba ne da suke samun tallafi daga ko’ina a Najeriya, mu ke daukar dawainiyar wasanninmu ba tare da tallafin kowa ba. Da haka muka tafi kasar Malesiya inda muka yi wasan share fage na shiga gasar kwallon dawaki ta duniya. Kuma muna sa ran za mu sake komawa don gudanar da wadansu wasannin. Kuma ina mai tabbatar maka da cewa mu ne muka dauki dawainiyar wasanninmu.Yanzu idan ana maganar wasan dawaki ana sanya Najeriya a cikin jerin kasashen da suka yi fice. Muna da Sanata Hadi Sirika shi ma dan wasanmu ne da sauran mutane masu yawa.