✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwallon da na jefa a ragar Jubentus ce ta fi ba ni sha’awa a rayuwata – Ronaldo

Shahararren dan kwallon Real Madrid na Sifen Cristiano Ronaldo ya ce kwallon da ya jefa a ragar kulob din Jubentus na Italiya a gasar cin…

Shahararren dan kwallon Real Madrid na Sifen Cristiano Ronaldo ya ce kwallon da ya jefa a ragar kulob din Jubentus na Italiya a gasar cin Kofin Zakarun Turai a ranar Talatar da ta gabata ce ta fi ba shi sha’awa a cikin dukan kwallayen da ya jefa a raga a daukacin rayuwarsa.

Cristiano Ronaldo wanda ya samu nasarar jefa kwallo biyu a ragar Jubentus a yayin wasan, ya nuna farin cikinsa da kwallon da ya jefa da taka-juye ne al’amarin da ya sa hatta magoya bayan Jubentus suka mike tsaye suna yi masa tafi saboda burge su da ya yi.

A wasan kulob din Real Madrid ne ya lallasa na Jubentus da ci 3-0.  A ranar Laraba mai zuwa ne kulob din biyu za su sake haduwa a karo na biyu a Sifen don tantance kungiyar za ta haye matakin kusa da na karshe  inda aka hada sakamakon wasannin biyu. 

Ronaldo, wanda ya taba jefa kwallaye masu ban sha’awa a lokuta daban-daban a baya, kamar wadda ya jefa a ragar Portsmouth tun daga tsakiyar fili a lokacin da yake kulob din Manchester United na Ingila da wacce ya jefa a ragar kulob din balencia da diddigen kafa da kwallon da ya zura a ragar Hungary a lokacin da yake yi wa Fotugal kwallo, duk ba su kai wacce ya zura a ragar Jubentus a ranar Talatar da ta wuce sha’awa ba, inji shi. 

“A gaskiya ba na jin akwai kwallon da na fi kauna irin wacce na zura a ragar Jubentus, hasali ma a ganina ita ce kwallon da na fi kauna a rayuwata”, inji shi.

dan shekara 33, Ronaldo tauraruwarsa na haskakawa wajen zura kwallaye a raga.  Hasali ma a bana babu dan kwallon da ya kama kafarsa wajen yawan zura kwallaye a raga a gasar, bayan ya zura kwallo 14.