✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalliya a lokacin zafi

Ko kun san cewa kwalliya da ababen maiko bai dace ba a wannan lokacin? Wannan lokacin zafi ne idan ana son kulawa da kurajen fuska…

Ko kun san cewa kwalliya da ababen maiko bai dace ba a wannan lokacin? Wannan lokacin zafi ne idan ana son kulawa da kurajen fuska da kuma hana wasu fitowa kamar su maruru da sauransu ya kamata a bi wadannan shawarwarin.

•Hoda:Idan za a yi amfani da hoda a tabbata cewa hodar ba ta da maiko. A yi amfani da hodar da za ta tsotse gumin fuska. Kuma ana amfani da kala mara duhu domin ta haskaka fuska.
•Ana amfani da prima kafin a dora hoda a fuska. Shi prima yana hana kwalliya bacewa da wuri, wato yana dan rike kwalliya.
•Kamar yadda a wannan lokacin ba za a so sanya bakaken kaya ba ko kuma kala masu duhu, haka fuskar ma ba komai za a shafa mata ba, sai a sama mata kala mai haske. Kada kuma a manta shafa hoda mai haske a kan hanci.
•A rage amfani da janbaki mai maiko domin zafin rana na sanya shi narkewa kuma hakan na bata kwalliya sosai.
•Kada a manta idan za a yi amfani da gazal ko kayan kwalliyar fuska, kamar su mascara da sauransu a yi amfani da wadanda idan ruwa ya taba ba zai bata kwalliya ba.
•Kuma ya kamata uwargida ta yi wanka a kalla sau biyu a rana.