✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwalin Digiri ba lasisin aiki ba ne – Mai digiri da ke sayar da dankali

Burina shi ne Allah Ya daukaka ni a wannan kasuwanci, in ci gaba da taimaka wa wasu.

Aminiya ta zanta da Faruk Rabilu Mai Dankali matashi dan shekara 27 da ke zaune a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, wanda ya yi karatu har matakin digiri amma ya kama kasuwancin sayar da dankalin turawa, inda yake shiga kauyuka yana sayo dankalin, yana kawowa garin Jos ya sayar.

Da farko za mu so mu ji tarihin rayuwarka.

An haife ni a nan garin Jos, shekara 27 da ta gabata. Na yi makarantar firamare da sakandare a nan garin Jos. Daga nan na tafi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na yi karatun digiri a fannin tarihi, na kammala a shekarar 2017. Daga nan na tafi aikin yi wa kasa hidima a Gombe.

A matsayinka na wanda ya yi karatun digiri a jami’a, mene ne ya karfafa maka gwiwar rungumar wannan kasuwanci, na sayar da dankalin turawa?

Ni dai tun lokacin da na taso ina yaro, ina zama a shagon babanmu da yake sayar da katifa ina ganin yadda ake yin kasuwanci.  

Da na kammala makaranta, sai na ga cewa shagon ba zai iya rike mu ba, sannan kuma ga kannena suna tasowa. Don haka na ga cewa ya kamata in bayar da waje in je in rike kaina.

Sai na fara bin wani abokina zuwa kasuwar ’yan tumatur da ke nan garin Jos, yana koya mani harkar kasuwancin gwari. Idan muka dawo gida, yakan dauki Naira 500 ya ba ni.

Wannan kasuwa muna zuwa sau uku ne a mako. Daga cikin kayan gwarin da yake turawa zuwa Kudancin kasar nan, akwai dankalin turawa kuma ana bukatar wannan dankali.

A duk mako muna sayen kamar buhu 15, mu tura. Kuma ni nake rubuta sunan wadanda za a kai wa wannan kaya.

Faruk mai dankali yana kama buhunan dalkalin da ya saya a kasuwar kauye

Daga nan sai muka yi shawara, tun da a duk mako muna sayen kamar buhu 15, mu tura. Don haka ya kamata na fara zuwa kasuwannin kauye da ake sayo wannan dankali, a garuruwa daban-daban na Jihar Filato.

Da muka yi wannan shawara sai muka samu dan karamin jari, na fara zuwa ina sayo wannan dankali buhu 5 zuwa buhu 6.

Idan na dawo nan Jos, na yi hoton wannan dankali na sanya a dandalin abokai na yanar gizo, mutane suna zuwa su saya.

Kuma ina ajiye wannan dankali a zauren gidan kakannina, idan aka zo saye sai in je in dauko.

Daga nan na samu shago na je na aro kudi, na biya kudin hayar wannan shago, bayan wata biyu na biya bashin da na karbo.

Na ci gaba da wannan harka ranar kasuwar Building Material da ke nan garin Jos na kai wannan dankali, ranar Kasuwa Farar Gada na kai wannan dankali kasuwar.

Daga nan abin yana bunkasa, domin duk wanda ya sayi kayana yana murna, don haka sai ya hada ni da wani, shi ma ya saya.

Kuma babban dalilin da ya sa na rungumi wannan kasuwanci, ba na son na zama rago. Na fi son in tashi in nemi na kaina.

Ganin ka yi makaranta har ka kai jami’a, shin ka nemi aikin gwamnati ne ko ba ka nema ba?

Gaskiya ina da abokai da dama da suka riga ni kammala karatun jami’a, kuma sun nemi aiki amma ba su samu ba.

Don haka sai na dauka a zuciyata cewa in Allah Ya yarda, idan na kammala makaranta ba zan tsaya wani neman aikin gwamnati ba, zan fara kasuwancina na kaina.

Kamar a wadanne wurare ne kake zuwa ka sayo wannan dankali?

Akwai kasuwannin dankali kamar guda biyar a nan Jihar Filato, da nake zuwa ina sayo dankali.

Ka ga akwai Kasuwar Mangu da take ci a duk ranar Juma’a, da Kasuwar Barikin Ladi da ke ci a duk ranar Asabar da Kasuwar Maikatako da take ci a duk ranar Litinin da Kasuwar Bokkos da ke ci a duk ranar Alhamis da kuma Kasuwar Amper da ke ci a duk ranar Talata.

Ina zuwa wadannan kasuwanni na sayo dankali na kawo nan cikin garin Jos.

Ganin ka yi karatu har ka kai ga digiri ba ka jin kunyar yin wannan kasuwanci?

Gaskiya ba na jin kunyar komai kan wannan kasuwanci, da nake yi. Saboda abokaina ma da suke aikin gwamnati, yawanci sukan biyo ni, kafin wata ya kare in saya masu katin waya, ko in ba su rancen kudi.

Don haka ba na jin nauyin wannan kasuwanci ko kadan.

Faruk mai dankali ana dora masa dankalin da ya saya a kasuwar kauye

Daga lokacin da ka fara wannan kasuwanci zuwa yanzu wadanne irin nasarori ne ka samu?  

Gaskiya na samu nasarori da dama. Domin tun daga lokacin da na fara wannan kasuwanci, ban taba rokon wani Naira daya ba.

A kullum ina samun duk abin da nake bukata a wannan kasuwanci. Sai dai ina ririta jarina da abin da nake samu saboda halin rayuwa.

Bayan haka wasu sun zo suna cin abinci a karkashina domin akwai wani abokina shi ma ya gama jami’a na jawo shi a wannan harka, yana taya ni.

Sannan kuma akwai kannena guda biyu da suke taimaka mani. Domin gaskiya yanzu aikin yana neman ya fara yi mani yawa, saboda tallata wannan kasuwanci da nake yi a kafofin sada zumunta.

Bayan haka ina dauke wasu hidimomi a gidan mahaifina, wani lokaci zan kai wani abu gidanmu sai na samu mahaifina ya kai, ba tare da na sani ba. Kadan daga cikin nasarorin da na samu ke nan, a wannan kasuwanci.

Mene ne babban burinka a wannan kasuwanci?

Babban burina shi ne Allah Ya daukaka ni a wannan kasuwanci, in ci gaba da taimaka wa wasu.

Ganin halin da ake ciki a kasar nan na rashin aikin yi, wane kira ne kake da shi zuwa ga matasa, musamman wadanda suka yi karatun boko?

Ina kira ga matasa musamman wadanda suka yi karatun boko su yi kokari su samu sana’ar yi. Kada su ce za su dogara da aikin gwamnati, su dage su nemi sana’a domin su kare mutumcinsu.

Faruk mai dankali ya dauko dankalin da ya saya a kasuwar kauye