Akalla gawarwaki 18 ne aka tsamo, wasu mutum shida kuma ake ci gaba da neman su bayan wani kwalekwale ya kife a Karamar Hukumar Mai’aduwa da ke Jihar Katsina.
Wani mazaunin yankin, Lawal Sakatare, wanda ya tabbatar da faruwar hatsarin ya ce kwalekwalen na dauke ne da mutum 24, akasarinsu kananan yara wadanda ke bukukuwan Sallah Karama, lokacin da ya gamu da iftila’in.
- ’Yan sanda sun fara neman masu lalata da karnuka a Legas ruwa a jallo
- 2023: Osinbajo ya sayi fom takararsa a APC na N100m
“Mutum 14 daga cikinsu ’yan kauyen Tsabu ne, hudu kuma ’yan kauyen Hawa ne. 14 daga cikin 18 din an binne su yau [Alhamis], yayin da ragowar mutum shidan da ke cikin jirgin har yanzu ake ci gaba da nemansu,” inji Lawal Sakatare.
Ya kara da cewa har yanzu ayarin masu aikin ceto daga yankunan na ta kokarin lalubo ragowar mutanen.
Sai dai ya ce fatan da ake da shi na samun su da rai ya ragu matuka.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar, SP Gambo Isa bai amsa kiran wayar wakilinmu ba ko amsa rubutaccen sakon da aka tura masa har zuwa lokacin hada wannan rahoton don jin ta bakin rundunar.