Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Yauri/Shanga/Ngaski na Jihar Kebbi, Yusuf Tanko Sununu, ya ce ’yan bindiga sun bar sako kafin su kai harin da suka sace dalibai da malaman Kwalejin Tarayya da ke Yauri.
A bayaninsa bayan harin da aka sace dalibai da malamai aka kuma kashe dan sanda tare da harbin wasu dalibai a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri, a ranar Alhamis, Dan Majalisar ya ce ’yan bindiga suna cin karensu babu babbaka a mazabar tasa.
- Saudiyya ta kashe matashi kan laifin da ya aikata yana karami
- ’Yan fim malamai ne masu koyar da tarbiyya, inji Saratu Zazzau
“Ko sati daya ba a yi ba da ’yan bindiga sama da 250 a kan babura suka shiga yankin suna bi har daki-daki suna kwace kudade da wayoyin hannu da dabbobi,” suka kuma bar sako cewa za su sake dawowa.
“Sun shafe sama da awa takwas suna cin karensu babu babbaka, wanda bayan haka ne mutane da dama suka yi gudun hijira zuwa Yauri,” inji Sununu.
Dan Majalisar ya ce da kyar, da ba da baki, aka samu wasu suka daga cikin mutanen suka yarda suka dawo garin da zama.
“Wasu mutanen da suka firgita da sakon ’yan bindiga kuma ba su koma ba; Yau da misalin karfe 10:30 na safe kuma sai ga shi sun sake kai irin harin wanda suka kai a baya,” inji shi.
Sununu ya ce a baya-bayan nan, yankin na Kudancin Jihar Kebbi ya yi fama da munanan abubuwa da suka lakume daruruwan rayuka.
“Ba a dade ba da mutum 154 a mazabata suka rasu a hatsarin jirgin ruwan da ya kife da su; gawarwaki 98 da mutum 28 daga cikinsu kadai aka gano.”