✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalara ta halaka daruruwan mutane a Arewa maso Gabas

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta (Norwegian Refugee Council (NRC), ta tabbatar da mutuwar mutane 175 da cutar kwalara ta halaka, a sansanonin ’yan…

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta (Norwegian Refugee Council (NRC), ta tabbatar da mutuwar mutane 175 da cutar kwalara ta halaka, a sansanonin ’yan gudun hijira dake Arewa maso Gabas da Boko Haram suka daidaita, tare da kwantar da mutane dubu 10 a asibitocin jihohin Adamawa da Borno da Yobe.

Malama Hauwa tana daya daga cikin mutanen da aka kwantar a Asbitin Kwararru dake Maiduguri, ta shaidawa wakilinmu irin halin da suka kasance a sansanin gudun hijira na Dalori a Maiduguri.

Inda ya bayyana cewa, “A gaskiya muna da matsalar rashin isassun bayan gida, da rashin wadataccen ruwan sha, a sakamakon haka ya sanya dole ta sa muke yawan samun matsaloli a wajen gudanar da harkokin rayuwarmu na yau da kullum, musamman ganin cewar akwai yara matasa maza da mata a cunkushe wuri guda.”

“Sannan ga kuma iyaye tsofaffi ga kuma kananan yara da jarirai a, amma a haka muke rayuwa da karancin ruwan sha da wuraren bahaya, wanda yake haifar mana da matsaloli da dama, musamman a yanzu da ya kashe wasunmu, mu kuma muke kwance a asbiti. Don ko mai gidana ma ya sallaci gawarwaki da dama, amma shi bai kamu da cutar ba, sai dai ni da ’ya’yana biyu, wanda daya ya rasu daya kuma muna tare da shi anan asibitin,” inji ta.

Ta kuma kara da cewa, a yanzu haka Alhamdulillahi, suna samun sauki a sakamakon kulawan da malaman asibitin ke yi masu da sauran wadansu kungiyoyin sa kai, sannan ta ce ana basu magunguna da sauran kayayyakin gina jiki. Daga nan sai ta roki gwamnati da ta tsamar dasu daga sake fadawa cikin irin wannan yanayin da suka samu kansu a sansanonin, wajen samar masu wadatacce kuma tsaftataccen ruwan sha tare da yawaita wuraren bahaya don gudun sake kamuwa da irin wannan cutar anan gaba.

Ita ma Shugabar Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA), Hajiya Yabawa Kolo, ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta kuma ce hukumarta za ta yi iya kokarinta wajen dakile cutar a sansanonin gudun hijiran da ya shafa, sannan kuma za ta ci gaba da taimaka wa wadanda suke kwance a asbitocin a halin yanzu.