✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwadayin nama

Wasu Hadejawa ne suka je bikin suna gidan wara Bagwariya, sai ta kawo musu nama, ta ce: “Ga shi dan kadan, amma kan kare ne.”…

Wasu Hadejawa ne suka je bikin suna gidan wara Bagwariya, sai ta kawo musu nama, ta ce: “Ga shi dan kadan, amma kan kare ne.” Su a zatonsu, matar tana nufin ‘kadan kankane.’ Ita kuwa tana nufin naman na kan kare ne. Hadejawan nan sai suka ce: “Ba damuwa, ai ba za mu raina ba.” Nan suka cinye nama tas, har da sude kwano. Bayan sun gama shi ne take cewa: “Ashe kuna cin kare, ga shi ma karami ne.” Nan take suka gane ashe kare take nufi. Nan suka fara kakari, wai suna son haraswa.”

Daga Maryam Idris Metu, 07038412210