✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kusancinmu da Abuja na jawo safarar yara – Al-Makura

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawa, ya bayyana damuwa dangane da yawan safarar kananan yara da a yanzu ya zama ruwan-dare a jihar, inda…

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawa, ya bayyana damuwa dangane da yawan safarar kananan yara da a yanzu ya zama ruwan-dare a jihar, inda ya alakanta aukuwar lamarin ga kusancin jihar da Birnin Tarayya, Abuja.

Gwamna Al-Makura ya bayyana haka ne  lokacin da yake karbar bakuncin Shugabar Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa, (NAPTIP) Dame Juliet Okah wace ta ziyarce shi a Gidan Gwamnati da ke Lafiya a karshen makon jiya. Ya ce matsalar safarar mutane a yanzu ta zama wata annoba da ke ci gaba da ci wa gwamnatinsa da sauran gwamnatocin kasar nan tuwo a kwarya idan aka yi la’akari da makudan kudi da gwamnatocin ke kashe wajen tunkarar lamarin.

Ya bayyana cewa “Ina sanar da ke cewa kasancewa muna kusa da Birnin Tarayya, Abuja, shi ya sa muka fi sauran jihohin kasar nan fuskantar safarar kananan yara da wadansu miyagun mutane da bincikenmu ya gano cewa galibinsu daga kasashen waje ne suke shigo wa kasar nan su yi. Ina tabbatar miki cewa a shirye gwamnatina take ta hada kai da hukumarki don tabbatar da cimma nasarar yaki da wannan muguwar dabi’a ta safarar yara a jihar nan da kasa baki daya. Kuma za mu duba dukan bukatun da hukumarki ta gabatar mana don yin wani abu a kai.”

Tun farko da take bayyana wa Gwamnan makasudin ziyarar, Shugabar Hukumar, NAPTIP, Dame Juliet Okah ta ce sun je jihar ce don su nemi gudunmawar fili daga gwamnatin jihar domin ba su damar gina makaranta don koyar da kananan yara da mata sana’o’i daban-daban da gina wuraren wasannin motsa jiki da sauransu domin a ba su damar dogara da kansu saboda hakan a zai taimaka wajen kare su daga sharrin masu safarar mutane a jihar da kasa baki daya.

Ta ce safarar mutane musamman kananan yara babban laifi ne da a yanzu ya kasance babban kalubale da barazana ga tsaron kasa. Shi ya sa a cewarta ya zame wa hukumar dole ta hada hannu da gwamnatocin jihohin kasar nan wajen tunkarar lamarin.

Daga nan sai ta yaba wa Gwamna Umaru Tanko Al-Makura dangane da aiwatar da muhimman shirye-shirye da suke inganta rayuwar al’ummar jihar musamman matasa wanda hakan a cewarta yana taimakawa matuka wajen ragewa da magance matsalar safarar mutane a jihar. Sa ta bukace shi da ya ci gaba da kyakkyawan aikin da yake yi.