✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Kusan sau miliyan 13 aka yi yunkurin yi wa Najeriya kutse yayin zaben Shugaban Kasa’

Minsitan Sadarwa Isa Ali Pantami ne ya sanar da hakan

Gwamnatin Tarayya ta ce akalla sau 12,988,978 aka yi yunkurin yin kutse a shafukan intanet na Najeriya yayin zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisun Tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan da ya gabata.

Hare-haren, a cewar gwamnatin an kai su ne daga ciki da wajen kasar, kuma an yi su ne kan shafukan gwamnati, kusan sau 1,550,000 a kullum.

Ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata.

To sai dai ya ce yunkurin kutsen ya yi tashin gwauron zabo zuwa sau 6,997,277, a ranar zaben Shugaban Kasa ta Asabar.

“Abin lura a nan shi ne cibiyoyinmu sun sami nasarar toshe dukkan wadannan yunkurin tare da mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar matakin da ya dace a kansu,” in ji Pantami.

Ministan ya kuma ce ma’aikatarsa ta kafa wani kwamitin yaki da irin wadannan hare-haren, kuma ya fara aiki ne ranar 24 ga watan na Fabrairu, sannan ya kammala ranar 28.