✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kurkum?!

Kurkum dai kwaramniyar kurum ce a wajen dandasa kwalliya da kwalisa da adon gari da iyayen giji ke yi, don su gyagije, su rika walwali…

Kurkum dai kwaramniyar kurum ce a wajen dandasa kwalliya da kwalisa da adon gari da iyayen giji ke yi, don su gyagije, su rika walwali da kawalniya. An kuma yi cikakken batu a kan wannan kalma, inda aka kalallameta a shafi na karamin lauje da tsayuwa bisa kafa daya na Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya cikin makon da ya arce.
Mu kuwa ’yan makaranta da ke koyon watsattsake a farfajiyar Dodorido, mun fasko cewa, kurkum kunkurun kurum ne da kwaramniyar kurum. Batuna dutse ne, domin na bijiro wa Dodanniya matar Dodo da tambaya game da kurkum, ita kuwa ta nusar da ni cewa, ai wani abu ne da ake dandansa kwalliya da shi, amma launinsa ya yi kama da na sinadarin inganta zaki da dandanon miya. Sai na ce, lallai uwargida kin yi batu mai kyau. Sai kuma ga shi da na tuntubi Hajiya Kanusiyya, matar Gizogizon-dakin-gwaggo, sai na ji wai murna take yi, ‘wai maigidanta ya sawo kurkum,’ amma ta ja masa na zomo, kan lallai kada ya kuskura ya kai wannan kurkum din can garin Masu-numfashi ko Masu-numfashi da ke cikin Jihar dakin-kara.’ Hajiya Kanusiyya ke da Man-kaza na bayan kango ku je can ku ci gaba da kunkurun-kurum, kuma ki sha kurumin ki, ina ganin idan kin dage maigida zai yiwo miki cefanen kurkum; ke kuwa ki yi ta kurme da kwaramniyar kwalliya a birnin Dabo inda ba adabo.
Haurobiyawa, mu bi kadin kwaramniyar kwaram da ke tafiyar kunkurun kurum a kasar mu ta-gado, amma ba ta gado (tsuntsu) ba.
Duk sa’adda aka yi batun dandasa kwalliya da kwalisa ko caba ado, ni ina ganin bai kyautu ba a ce mutanen Tumfafi sai sun yi ado da tumfafiya ba. Wanda duk ya mallaki malum-malum ko jubba da kufta ko jallabiya ya iya yafawa ya tafi wurin kwadago don neman kadago. Idan kuwa uwargida ce sai ta ci dammara da zane ta kanannade jiki da laffaya, amma ba ta sanya shimi, ta fito a titi tana shirme ba. Kai wata ma har da dan guntun buje za ka ga ta kakaba iya kwauri, wai ita ta cinye, sai ka ce Baturiya. Ko dayake namiji ma wani sai ka ga ya yi tukunyar dambu, ya shake wuya da raga; wai ya taho yana taku irin na masu gingimarin kurunku, alhali kai ba farar fata ba.
Yanzu haka ma wancan dan gidan mai motar roba sai ka ga yana rangwada irin ta ’yan matan Turawa, amma idan ka tambaye shi sunan Maimotar roba da Ingilishi, sai dai ya murguda baki kamar yana cin kilishi, a,mma ba shi da gilashin fasko matsayin kalmomi, illa dai kawai ya yi ta kwaramniyar kurum tamfar ya shafa kurkum.
dan gidan Maimotar roba ka sani, mu ma da muka iya Turancin sunan Maimotar roba na da wahalar furtawa, domin cewa ka yi: “ROBORIOUS MOTORIOUS, ko RUBBER ROBOTIC MOTORISED CAR.” Saboda haka ka koyi murguda baki kamar ka ci kilishi, ka kan ga gilashi, sannan ka yi ta yaren Ingilishi, amma ba ka yi tukunyar dambu ba, ko ka shake wuya da raga, sannan ka dambara kurkukum, wai da sunan kwaramniyar kwalliya da kwalisar ’yan gayun Turawa; idan na Faranshi ne, sai mu ce farashinka ya karu; idan kuwa na Ingilisdhi ne, sai kange ka da gilashi, mu dumdume maka kururu da kilishi, har sai ka samu kuzarin yin kilisa.
Kai ni fa yau kwaramniyata kawai nike yi, da taku irin na kunkurunkurum, sai dai kawai ni ba na dambara kurkum. Abin da kawai zan ce wa dimbin al’ummar Haurobiya, musamman masu laluben na koko ko kadago a wajen kwadago, batu ne da ya shahara a wakar Babbban mutum mai rawani a harkar dukan taushi, ga abin da marigayi Mamman na birnin Dikko:
“Nufin su mu (yi) was an gargajiya,
Ya sa mu kara fahimtar juna,
Wasu sun bar AL’ADU na IYAYEN SU, su bi na ‘YAN CIRANI!
Wannan kwaramniyar tawa na fasko cewa, za ta iya kai ni in gana da Ministan masu tashi da fuka-fuki, wato Malam Dalung, in ce masa ni ne dodong, na kuma taba ziyartar shagon mutanen Mao Zedong, wanda aka yi wa lakabi da Dung fong. Da na dawo Haurubja sai na umarci msu shagon nan kan cewa, lallai kada su sayar wa Gizagong Wandong.
A darasin mu na Salon Sallau-lado na bijiro muku da batutuwa kan yadda farfesa Sallau -lado ya yi hasashen kasancewar Haurobiya kasar Sin ta Ifrikiyya, ni kuwa na ce ta kusa karkewa da zama “SANSANIN SANE,’ ba cin Mai-duka ya kawo mana dauki mun samu Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajo da an ci gaba da kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma.
Kwaramniya da salon tafiyar kunkurunkurum da ake yi a Haurobiya ba za a taka burki ba, har sai mun zare wa Saurin-kirinki na-mujiya, mu azazzalin Dogarin wakilan rafkiya su aiki tukuru, ta yadda jam’iyya mai maganin zogi da radaddin ciwon kurungu da ya addabi al’ummar Haurobiya.
Ni dai kwaramniyata kawai nike yi, tare da kurme a cikin kwamin kunkurunkurum
Kurkum! Kurkum!! Kurkum!!
Dodo dan gaye ne
GizBaba dan kauye ne
Yana ninkayar kurme da sana’ar su
Burdigau sunan kauyen su
Can ba a kyarar sususu!
Lallai akwai bukatar a cusa kurkum cikin kurmusun kalmomin kamus, tunda mun kurmusa Jamus a kamus. Abin da ya san a bijiro da wannan bukatar, shi ne, a kowace shekara ana kara cusa kalmomi a Kundin Dogon-mutumin Ingilishi (LONGMAN) da kundin Babban dan koyo (ADbANCE LEARNER).  Kun ga ke bai kyautu ba, a ce KURKUM an barta a matsayin kwaramniyar kwalliya da caba ado kawai ba. Domin idan aka ci gaba da dambara kurkum alhali ba shi da gurbi a kurmusu kalmomin Jamus a kamus, sai kawai in umarci ’yan makaranta su kurmushe shi.
Batu na ingarman kwangiri, ba zan karkare kwaramniyata ba a wannan makon, har sai na ja na-zomon GizBaba da dan gidan Maimotar roba kan lallai su saya wa matan su kurkum don su dan dasa kwalliya. Uwa-uba Baban-burin-huriyya da Usaionin-Babajo su daina bari Saurin-kirinki da Dogarin wakilan rafkiya na yi musu kwaramniyar kurum da tafiyar kunkunrun kurum, ta yadda Haurobiya za ta zama cikin gungun ‘’yan gayu, ba wata yawa, ko e, yane- yane!