✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

 Kurame Sun Bukaci A Gina Musu Makarantar Kwana A Damaturu

Kurame Musulmi (ADMUN) sun roki gwamnati ta gina makarantar musamman ta kurame a Damaturu

Kungiyar Kurame Musulmi a Najeriya (ADMUN) ta roki gwamnatin Yobe da ta tarayya da su gina makarantar musamman ta kurame a Damaturu, babban birnin jihar.

Mataimakin shugaban kungiyar, Mohammed Abubakar Sadiq ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida game da taron da’awa na shekara-shekara karo na 32 da kuma taron kurame na kasa a Najeriya da suke gudanarwa a Damaturu.

Taron mai taken, “Kalubalen da ake fuskanta a rayuwar kurame Musulmi ” na gudana ne a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Damaturu.

Sadiq ya ce makasudin da’awar da shirye-shiryen taron “shi ne yada ilimin addinin Musulunci a fadin Najeriya.”

Ya bukaci jama’a da su sani cewa kungiyar “tana gudanar da tarukanta a duk shekara” kuma akwai kalubale da dama da suke fuskanta musamman a bangaren samar da kudade.

“Mutane da yawa sun yi alkawarin taimaka mana, amma sun kasa cika alkawuran da suka dauka.

“Don haka ina kira ga gwamnati ta duba mu domin mu ga karshen wadannan matsalioli cikin nasara.

“Sauran kalubalen da muke fuskanta shi ne ta fannin ilimi;  mun ba da shawarar gina mama makarantar kwana a babban birnin jihar Yobe kana kurame ba su da wani aiki kuma har yanzu ba a yi komai ba ta fuskar taimako,” inji shi.