✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kura da kunkuru

Kura ce ta kama kunkuru sai ta yi ta kokari ya cinye shi amma ta kasa. Sai ta ce masa: “Wai kai yaya ake cin…

Kura ce ta kama kunkuru sai ta yi ta kokari ya cinye shi amma ta kasa. Sai ta ce masa: “Wai kai yaya ake cin ka ne?” Kunkuru ya ce: “Ai sai an jika ni a ruwa tukunna.” Kura ta jefa shi a ruwa, ta koma gefe ta yi ta jira. Da ta ga shiru sai ta ce: “Wai ba ka jiku ba ne?” Kunkuru ya ce: “Wawiya! Ai nan gidana ne.”
Daga Yusuf Double Sense Maiduguri, 07034506944