Wata kungiyar kwararru kan harkar kiwon lafiya a karkara mai suna Rural Health Mission (RHM) da Kungiyar Ci gaban garin Lawanti, (Lawanti Community Debelopment Foundation- LCDF) da tallafin dan Majalisar Jihar mai wakiltar mazabar Akko ta Yamma, Alhaji Yahaya Muhammad Kaka, sun ba al’ummar garin Zangomari a Karamar Hukumar Akko, magani kyauta.
Da yake zantawa da Aminiya lokacin aikin bada magani kyauta Shugaban Kungiyar Rural Health Mission a Gombe, Muhammad Sadik, cewa ya yi suna yin irin wannan aiki jinya a kauyuka kyauta idan kungiyoyin al’umma suka hada kai da su kamar yadda kungiyar ci gaban garin Lawanti ta yi.
Muhammad Sadik, ya ce kudirinsu a kwana daya da za su duba marasa lafiya shi ne suna sa ran ganin majinyata kimanin dubu daya su ba su magani domin suna da isassun ma’aikatan jinya da suka kai 30.
Ya ce cututtukan da suka fi mayar da hankali a kai su ne zazzabin Typhoid da maleriya wadanda su ne suka fi addabar mutane da hawan jini da ciwon sukari da ciwon hanta da sauransu ba kawai iya wadannan suke dubawa ba; a’a kowace irin cuta suna dubawa har da ciwon ido sun bada gilashi kyauta.
Sadik, ya ce idan suka samu cutar da ta gagare su suna iya tura majinyacin babban asibiti inda suke da hadaka irin wannan da su domin a duba marar lafiyar.
Ya yi kira ga masu hannu da shuni da shugabanni su rika tallafa wa marasa galihu wajen kula da lafiyarsu, musamman al’ummar karkara wadanda wadansu kudin mota na zuwa gwaji a asibiti ba su da shi balle kudin jinya.
Dan majalisar da ya taimaka wa shirin, Yahaya Muhammad Kaka, ya ce dama al’umma sun zabe su ne domin su yi musu aiki shi ya sa shi kuma ya ga dacewar taimaka wa al’ummar ta bangarori daban-daban da suka hada da na kiwon lafiya.
Shi ma a nasa tsokaci Shugaban Kungiyar LCDF, Malam Abu Ubaida cewa ya yi sun shirya wannan aikin jinya kyauta ne don taimaka wa al’ummar garin Zangomari.
Malam Abu Ubaida, ya ce a kungiyance za su yi bakin kokarinsu wajen ganin sun taimaka wa majiyata tun daga karamar cutar zuwa babba saboda ganin yadda ake yawan samun cututtuka.
Hakimin Zangomari, Alhaji Waziri Saleh, ya bayyana farin cikinsa ga kungiyoyi kan yadda suka zabi garinsa domin cin moriyar wannan shiri na kiwon lafiya kyauta.
Wadansu da suka ci gajiyar tallafin, A’isha Muhammad, ta ce ta bi layi likita ya duba ta kan matsalar hawan jini da olsa, aka kuma ba ta magani kyauta.
Muhammad Madugu, cewa ya yi zuwan ma’aikatan jinya ya taimaka musu domin akwai da yawa da suke fama da matsaloli amma rashin kudin zuwa asibiti yana damunsu sai ga magani ya zo musu har gida a gwada mutum a ba shi magani kyauta, ba su da abin cewa sai godiya.