✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyoyin da Messi bai taba jefa musu kwallo ba

Duk da iya murza leda da kwazo da ficen da dan wasan gaban na Barcelona Lionel Messi ya yi akwai kungiyoyin da har yanzu ya…

Duk da iya murza leda da kwazo da ficen da dan wasan gaban na Barcelona Lionel Messi ya yi akwai kungiyoyin da har yanzu ya kasa jefa kwallo musu kwallo a raga. Kafin wasan da aka buga a tsakanin Barca da Chelsea a ranar Talatar da ta gabata, kungiyoyin kwallon kafa 12 da suka hada da Chelsea ne Messi ya gaza ci, duk da kasancewarsa cikin ’yan kwallon da suka fi jefa kwallo a raga a duniya inda ya jagorancin kungiyarsa ta Barcelona ga doke kungiyoyi da dama, har ta zama jagora a fagen kwallon kafa a Nahiyar Turai.

Yanzu da Messi ya jefa kwallo a ragar Chelsea ya rage adadin kungiyoyin da bai taba jefa musu kwallo a raga ba zuwa 11, tun lokacin da ya fara wasa a babbar kungiyar Barca yana da shekara 17 a watan Oktoban, 2004, wato shekara 13 da rabi. Ga sauran kungiyoyin da Messi ya kasa ci a kasa:

Gramenet 

Bayyanar Messi a karo na uku kuma a jerin farko na ’yan wasan Barcelona ya zo ne a daidai lokacin da ya fara shan kashi lokacin da yaran na Frank Rijkaard suka hadu da rashin nasara a hannun Gramenet a gasar cin kofin Copa del Rey. Duk da akwai Messi da Henrik Larsson da Andres Iniesta a jerin farko na ’yan wasa 11, Barca ta gaza keta ragar kungiyar da ke rukuni na uku na ’yan dagaji, inda su kuma suka keta ragar Barca a karin lokaci. Kuma wannan ne kawai lokacin da Messi ya hadu da makwabtan nasu.

Udinese 

Yana da kwallo daya a Camp Nou, Messi yana nesa da tafiyar da za ta kai shi ga samun lambar zakaran kwallo na duniya har sau 5, lokacin da aka sa shi don fafatawa da kungiyar Udinese a Satumban 2005.

Amma a lokacin yana matashi mai kazar-kazar da ke buga wasa a gaba tare da su Ronaldinho da Samuel Eto’o.

dan wasan na Brazil wato Ronaldinho ne ya nuna cewa shi ne gwarzo a gasar ta Zakarun Turai,  inda ya jefa kwallo uku a wasan da suka ci 4-1.

Messi, a lokacin an cire shi daga wasa a minti na 70, kuma duk da ya jefa kwallo a wasa na gaba, amma an hutar da shi a wasanni biyu da suka biyo baya, wanda daya daga cikinsu har da sake fafatawa da Udinese.

Cadiz 

A watan Disamban 2005, Messi ya yi barin damarmakin da ya samu na daukaka sunansa a jerin kungiyoyin da ya fasa wa raga lokacin wasansu da Cadiz. dan wasan na Ajentina ya taimaka Barca ta samu nasara da ci 3-1, inda ya a farkon rabin lokaci na biyu ya ba Samuel Eto’o kwallo ya jefa a raga.

Kuma lokacin da kungiyoyin biyu suka sake haduwa Messi ya samu rauni, sai Ronaldinho ne ya jefa kwallon da ta ba Barca damar lashe gasar. Tun lokacin har zuwa yau ba su sake haduwa ba.

Real Murcia 

Kakar wasa ta 2007-2008, ta kasance abar takaici ga Barcelona, inda ta kare a ta uku a teburin La Liga da tazarar maki 18 tsakaninta da zakarar gasar Real Madrid. Sai dai ta buga wasa mai kayatarwa, inda bayan zura mata kwallo daya a raga ta fanshe tare da cin Real Murcia 5-1 a wasansu na karshe. Messi ya taimaka an ci kwallo biyu, amma Giobani dos Santos ne ya burge ’yan kallo inda ya jefa kwallo uku a raga. Kuma yayin da Barca ta fafata da Murcia a lokuta da dama, Messi bai buga ko daya daga cikin wasannin ba.

Al Sadd 

Barca ta samu nasara a gasar Club World Cup a shekarar 2011 da ci 4-0 a kan Al Sadd. Kuma duk da cewa Messi ya danne hasken dan wasan nan mai tashe, Neymar ta hanyar jefa kwallo sau biyu a gasar, amma ya kasa keta ragar Al Sadd a wasan kusa da na karshe, amma ya taimaka wa  Seydou Keita wajen ciyo wa Barca kwallo ta uku.

Girona 

Messi bai taka rawar gani ba a wasansu da Girona wadda ta samu shiga rukunin La Liga a bana. Barca ta samu kwallo biyu a bagas daga cin kansu da ’yan Girona suka yi, kafin Luis Suarez ya sake fasalin wasan. Messi ya rage adadin kungiyoyin da ya gaza keta ragarsu daga 12 zuwa 11 a wannan mako, idan ya jefa kwallo a ragar Chelsea a gasar Zakarun Turai a ranar Talatar da ta gabata, kuma yana iya rage adadin zuwa kungiyoyin 10 a gobe Asabar idan suka fafata da Girona a gasar La Liga.

Liberpool 

Messi da Ronaldinho da dabi da Deco suna iya hana Liberpool zuwa wasan karshe na Zakarun Turai a shekarar 2007 lokacin da suka hadu a wasan zagaye na biyu. Sai dai yaran Rafael Benitez sun samu nasara a kan Barca da ci 2-1 a gidanta na Camp Nou kafin su yi waje da Barca da ci 1-0 a wasansu na gaba. Kuma duk da cewa da Messi aka fara wasan aka kare, ya gaza jefa kwallon da za ta tsallakar da yaran na Rijkaard. Kuma ’yan wasan Anfield sun ci sa’a ba su sake haduwa da shi ba har shekara 11 tun daga lokacin.

Benfica 

Barcelona ta fafata ne da Benfica a farkon tashen Messi, inda ta doke kungiyar ta Portugala a wasan kwata-fainal a hanyarsu ta samun nasara a gasar Zakarun Turai a shekarar 2006.

Sai dai dan kwallon bai buga wasan ba, saboda rauni, kuma bai sake samun zarafin haduwa da su ba, sai a shekarar 2013, inda ya taimaka aka ci su 2, sai dai bai samu nasarar keta ragar Benfica duk da ya yi yunkurin haka sai biyu.

Derez 

Duk da Messi ya hadu da kungiyar sau biyu a gasar La Liga daga shekarar 2009 zuwa 2010, bai jefa kwallo a ragarsu ba, kuma an sanya shi ne bayan dawowa hutun rabin lokaci a duka lokutan.

Inter 

Lokacin Jose Mourinho yana horar da Inter Milan ne ya hana Barca daukar Kofin Zakarun Turai, lokacin da suka yi waje da Catalan din a wasan da ya ba kowa mamaki a wasan kusa-da-na-karshe a shekarar 2010.

kungiyoyin biyu sun hadu sau hudu a gasar, tun daga matakin rukuni, amma aka hana Messi sakat a bugawa uku da ya yi a shekarar.

Rubin Kazan 

kungiyar ta kasar Rasha, Rubin Kazan ta nuna ba kanwar lasa ba ce, a duk lokacin da ta hadu da Blaugrana kamar yadda ake kiran Barca. Domin duk da karfin kai hari da Gwarzon kwallon Duniyar sau biyar ke da shi, ya gaza samun nasarar keta ragarta a duk haduwar da suka yi. Bilhasali ma sau daya dan Ajantina ya samu nasara a kan Rubin a lokuta hudu da suka hadu da ita.