Gamayyar Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’Adama (CSOs) na kudancin Kaduna ta yi kira ga ‘yan yankin da su rika taimaka wa jami’an tsaro da sahihan bayanai.
Shugaban Kungiyar Southern Kaduna Indigenous Peace Practitioners (SOKIPEP), Dauda Fadia, ya ce jami’an tsaro na kokawa kan yadda ake ba su bayanan karya, wanda hakan ba ya taimaka musu wajen gudanar da aikinsu.
“Muna da labarin sojoji na kai dauki cikin hanzari idan aka kira su amma sai su tarar bayanin da aka basu ba gaskiya ba ne. Hakan ba ya taimaka wa yunkurinsu na kawo karshen kashe-kashen”, inji shi.
Dauda Fadia ya ce jami’an tsaro na iya kawo karshen dauki daidayan da ake yi a yankin idan har za a sama musu bayanan gaskiya a kan lokaci.
Sanarwar da ya fitar ta kara wa sojoji kwarin gwiwa na ci gaba da samar da doka a kudancin Kaduna, ya kuma soki korafin wata kungiyar mata da ta zargi sojoji da hannu a kashe-kashe a yankin.
Ya ce sojin na iya kokarinsu kuma kamata ya yi a kara musu kwarin gwiwa, inda ya gode musu kan zaman lafiyar da aka fara samu a yankin a kwanan nan.
Ya yi kira garesu da su gurfanar tare da mika wa ‘yansanda mutanen da ke hannunsu da ake zargin suna da hannu a rikice-rikicen da ke faruwa a kudancin Kaduna.