Shugaban kungiyar Masu Maganin Gargajiya ta kasa reshen Jihar Bauchi (BUNANTMP), Dokta Gambo Abdullahi Bababa ya ce kungiyar ta kudiri aniyar tsabtace sana’ar bayar da magungunan gargajiya a jihar. Dokta Gambo Bababa ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu, inda ya ce ganin yadda mutane da dama da ba su san harkar maganin gargajiya ba suke shiga sana’ar inda suke bata harkar ya zama wajibi su dauki matakin tsabtace sana’ar don kare mutuncin sana’ar. “Yanzu lamarin ya kai matakin da mutum zai debo itatuwa a daji ya shiga daki ya tsara talla a kaset ya kururuta maganinsa ya zo ya ba samari da kananan yara maganin da kaset-kaset din tallar suna zagaya gari suna sayarwa alhali shi kansa ba ya da kwarewa ko ilimi a harkar magannin gargajiyar,” inji shi.
Dokta Bababa ya ce, yanzu haka a kokarinsu na tsabtace harkar magungunan gargajiyar sun fara amfani da ’yan sandan ciki na kungiyar domin zakulo masu damfarar jama’a da sunan su masu magungunan gargajiya ne a jihar. Ya ce sun dauki wannan mataki ne bayan da suka rika samun korafi daga jama’a cewa wadansu masu magungunan gargajiya suna damfararsu. Ya ce duk wanda suka kama yana damfarar jama’a da sunan wannan sana’a za su mika shi ga hukuma domin daukar mataki a kansa.
Shugaban ya ce galibin masu fakewa da sana’ar magungunan gargajiya suna cutar mutane ba su da rajista da kungiyarsu ko wata kungiyar masu maganin gargajiya da hukumar lafiya ko wata hukuma ta yarda da ita. Ya ce, a kokarinsu na tsabtace harkar magungunan gargajiya da kare martabar sana’ar, tuni sun dakatar da wani jigo a kungiyar da ke jihar, inda ya yi fata masu magungunan gargajiya za su ba su hadin kai don kare martabarsu da kuma kiyaye lafiyar jama’a.