Shugabar kungiyar Matan Kwarai ta Jihar Kano ta ce kungiyarsu tana kokari wajen kyautata tarbiyyar matasa da magance halayyar shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran kayan maye.
Shugabar kungiyar Hajiya Maijidda Idris ce ta bayyana hakan ga Aminiya. Ta ce kungiyar tana bai wa mata horo kan sana’oi na dogaro da kai tare da ba da darussa ga mata kan ilimin addinin Musulunci da kuma na zamani, ta yadda al’amura za su inganta a tsakanin iyalai.
Daga nan ta bayyana cewa kungiyar tana da shugabanci a duka kananan Hukumomin Jihar Kano da kuma mambobi masu tarin yawa wadanda ake haduwa domin taimakon juna kodayaushe. “Har ila yau, muna shirya tarurrukan karawa mata ilimi kan duk wani al’amari na gwamnati kamar rigakafin cutar Shan Inna da zuwa awon ciki da kula da yara mata da kuma wayar da kan mata kan sha’anin zabe ko wani shiri na gwamnati,” inji ta.
Dangane da gyaran tarbiyya, Hajiya Maijidda tayi kira ga iyaye maza da mata dasu kara kokari wajen ba da “tarbiyya mai kyau ga iyalin su da lura da al’amuransu na yau da kullum domin kaucewa fadawa cikin rashin tarbiyya tun daga kuruciya musamman ma idan aka yi la’akari da maganar da ke cewa Ice tun yana danye ake tankwara shi.”
Daga karshe ta bukaci “daukacin mambobin wannan kungiya da su kara zage damtse wajen ganin al’umar Jihar Kano suna cin moriyar kungiyar musamman ganin yadda take da manufofi kyawawa na inganta zamantakewar iyali a kowane lungu da sako na jihar.”