✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘kungiyarmu ta raba bashin motocin noma sama da 200’

Ma’ajin kungiyar masu taraktocin noma da tukawa na kasa (TOOAN) kuma mai ba ministan gona shawara na musamman, Alhaji Hassan Malami Saminaka ya ce kungiyarsu…

Ma’ajin kungiyar masu taraktocin noma da tukawa na kasa (TOOAN) kuma mai ba ministan gona shawara na musamman, Alhaji Hassan Malami Saminaka ya ce kungiyarsu ta ba manoma bashin taraktocin noma sama da 200 a jihohi 25 na kasar nan. 

Ya ce hakan ne a lokacin da yake zantawa da Wakilin Aminiya a Saminaka da ke Jihar Kaduna a ranar Talata.
Ya ce sun fara wannan shirin ne da Jihar Ogun a shekarar 2006, inda suka raba bashin taraktoci guda 14. Daga nan suka zo Jihar Kaduna suka raba bashin taraktoci guda 36.
Ya ce “Bankin Duniya ya shiga cikin wannan shiri, inda suka tallafa wa duk manomi aka ba bashin tarakta da kashi 20 cikin 100 na kudin da zai biya, wanda ya kai Naira dubu 745.”
Ya ce suna amfani da bankunan First Bank da Eco bank ne wajen bayar da wannan rance.
Ya ce a yanzu manoman da suka ba rancen taraktocin noman wadansu sun zama manyan manoma. Domin ada wasu suna noma kamar buhu 50 zuwa 100 ne, amma a yanzu suna noma kamar buhu 1000.
Ya ce babban burinsu shi ne su bayar gudunmawarsu wajen bunkasa harkokin noma a Najeriya ta hanyar tallafa wa manoma manya da kanana.
Ya ce “Ganin irin kokarin da kungiyarmu take yi, ya sanya Ministan aikin gona ya dauke ni a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan aikin noma.”
Ya ce don haka Gwamnatin Tarayya ta hada hannu da kungiyar wajen bayar da rancen taraktocin noma da za ta yi nan ba da dadewa ba.
Ya ce duk manomin da za a ba bashin tarakta na gwamnatin tarayya, zai yi aiki ne da tsarin wannan kungiya.
“Gwamnatin Tarayya za ta bude wasu cibiyoyin noma guda 80 a kowane bangare na kasar nan. Za a ba kowace cibiya taraktocin noma guda 5 da sauran kayayyakin aikin gona guda 22.” Inji shi
Ya ce a duk inda aka bude wannan cibiya kananan manoma za su rika zuwa su yi magana aje a yi musu aiki kan kudi kalilan.
Ya yi kira ga manoman kasar nan su yi kokari su hada kai da wannan kungiya don su amfana da ayyukan kungiyar.