Shugabar Kungiyar Hadin Kan Zawarawa ta Jihar Gombe, Malama Fatima Abdullahi, ta ce suna neman tallafin gwamnatin jihar domin taimaka wa mata zawarawa ta hanyar dogaro da kai.
Shugabar ta ce kungiyar tasu tana da rajista da gwamnati inda take fadi-tashin ganin an taimaka wa mata zawarawa domin samun hanyar dogaro da kai har lokacin da za su yi aure.
“Muna hada kan zawarawa muna yi musu bita da fadakar da su hanyar zamantakewar yau da gobe don rage yawan mace-macen aure a tsakanin ma’aurata,” inji Shugabar.
A cewarta, kungiyar tasu tana tare da gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya, inda suka yi ta fadi-tashi tun lokacin yakin neman zave har aka kafa gwamnati.
Fatima Abdullahi, ta kara da cewa cikin irin aikace-aikacen kungiyar tasu har da hada karfi da karfe wajen yi wa zawarawan kayan daki su aurar da su.
Sai dai ta koka kan yadda kungiyar ba ta samu cin gajiyar masu bayin bishiyoyi da gwamnatin ta dauka su dubu 27 daga kungiyoyi daban-daban ba, kuma ta ce hakan ba zai sa su daina yi wa gwamnati biyayya ba, idan da rabonsu gaba za su samu.
Daga nan sai ta yi kira ga mambobin kungiyar su kara hakuri wata rana za a yi da su in Allah Ya yarda.