✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar ’yan kasuwar Kebbi ta zabi sabbi shugabanni

A ranar Litinin da ta gabata ne Hadaddiyar kungiyar ’Yan Kasuwan Jihar Kebbi ta kaddamar da sabbin shugabaninta, a taron da aka gudanar  a bakin…

A ranar Litinin da ta gabata ne Hadaddiyar kungiyar ’Yan Kasuwan Jihar Kebbi ta kaddamar da sabbin shugabaninta, a taron da aka gudanar  a bakin ofishin ’yan kasuwa da ke babbar kasuwar Birnin Kebbi.
Sabbin shugabannin sun hada da Alhaji Umaru dan-Gura  Gwadangaji a matsayin shugaba, da Alhaji Shehu Mai Fulani  a matsayin mataimakin shugaba da Alhaji Bello Kalgo a matsayin janar sakataren da kuma Alhaji Amadu Mai Turare wanda shi ne sabon ma’ajin kungiyar.
Sabon shugaban ya bukaci gwamnatin Jihar Kebbi karkashin jagorancin Sanata  Abubakar Atiku Bagudu, a dukkan matakai, su rika ware wa fannin kasuwanci wani kaso na musamman, wanda zai taimakawa ’yan kasuwa wajen farfado da tattalin arziki.
Daga nan ya jaddada cewa ’yan kasuwa na taka muhimmiyar rawar samar da hajoji a wuraren da ake bukata, “don  haka yakamata gwamnatoci su rika bayar da gudunmuwa don samar da kayayyaki cikin farashi mai rahusa ga jama’a,”  inji shi.
Har ila yau, ya yi kira ga ’yan kasuwa su ci gaba da nuna halayen kwarai ga duk wadanda suke hulda da su .
“Duk dan kasuwa da yake kamanta gaskiya a harkokinsa, ya fi samun abokan hulda da kuma bunkasar harkokinsa cikin lokaci kankane, sannan zai samu babbabn rabo daga Allah, kuma Ya albarkaci dukiyarsa,” inji shi.
A karshe Alhaji dan-Gora ya yi alkawarin za su kamanta adalci  wajen gudanar da nauyin da aka dora masu saboda haka ya jawo hankalin ’yan kungiyar su kasance masu gaskiya da rikon amana da biyayya ga shugabanni.