Shugaban kungiyar ‘yan Jarida na kasa reshen Jihar Bauchi Malam Ibrahim Malam Goje ya jagoranci shugabanni da kuma membobin kungiyar NUJ reshen Jihar Bauchi, ziyarar taya murna da kuma ganewa ido sabuwar gidan rediyon da aka kafa a Jihar Bauchi mai suna Albarka.
Shi dai Rediyon Albarka mallakar tsohon Darekta Janar na Gidan Rediyon Tarayya FRCN Mallam Ladan Salihu ne, kuma yanzu haka an budeshi ya na kan gwajin shirye shiryensa, inda ake kamashi kan FM 97.5 kimanin makonni uku da suka wuce.
Da yake jawabin, Shugaban, Ibrahim Mallam Goje ya ce samar da wannan sabon gidan rediyon a Bauchi babban ci gaba ne ga Jihar Bauchi, dominn banda gidan Rediyon Raypower FM babu wata kafar yada labarai a jihar mai zaman kanta, kuma kafar sadarwa mai zaman kanta zai taimaka wa jama’a wajen fadin ra’ayoyin su da kuma fadar abin da ke cikin ransu tunda ba komai ne mutum zai iya fayyacewa a gidan rediyo mallakar gwamnati ba.
Mallam Goje ya kuma shawarci ma’aikatan sabon gidan rediyon da cewa su tabbatar da yin aikinsu cikin kwarewa, da bin dokokin aikin jarida, ya horesu da su kauraracewa fita daga cikin ka’idojin aikin jarida, sannan ya yi kira ga hukumar gidan rediyon da su bi dokoki da ka’idojin da Hukumar Kula da kafafen yada labarai wato (NBC) ta shimfida, sannan ya gargadesu da su guji kaucewa hanya ko son zuciya a fagen aikinsu na jarida.
Shugaban NUJ ya yi alkawarin cewa nan ba da jimawa ba, za a kirkiro masu sabuwar reshen kungiyar na gidan rediyon, kamar yadda kowace kafar sadarwa ke da rassa a jikin uwar kungiyar, domin su zama cikakkun membobin NUJ. Sannan sai ya yi kira ga ‘yan asalin Jihar Bauchi masu hannu da shuni da su tabbatar da yin koyi da irin su Ladan Salihu wajen kawo abubuwan cigaba a Jihar Bauci domin inganta tattalin arzikin jihar da kuma bunkasa ci gaban jihar a kowane lokaci.
A jawabinsa, Ladan Salihu ya bayyana mutukar farin cikinsa da kuma godiyarsa a bisa ziyarar da NUJ ta kawo masu, sai kuma ya yi alkawarin yin aiki da shawarwarin da aka basu.
Salihu ya bayyana cewa sun kafa wannan tashar rediyon ne a Bauchi ne a maimakon Abuja domin a bai wa jama’a damar bayyana ra’ayoyinsu da kuma inganta aikin jarida da ‘yan jarida masu tasowa nan gaba.
Haka shi ma Janar Manaja na gidan rediyon Albarka Alhaji Musa Waziri ya shaida wa kungiyar cewa za su tabbatar duk wani ma’aikacinsu yana bin dokoki da kuma ka’idar aikin jarida. Sannan ya ce ma’aikatansa za su yi biyayya domin gudanar da aiki yadda ya dace cikin kwarewa da sanin ya kamata kamar yadda yake a tsarin aikin jarida.