Kungiyar ’Yan fansho ta Kasa reshen Jihar Kebbi ta zabi sababbin shugabannin da za su ja akalar kungiyar.
An gudanar da zaben shugabannin ne a dakin taro na Makarantar Koyon Aikin Jinya da Ungozoma da ke garin Birnin Kebbi, inda aka samu ’yan takarar neman shugabancin kungiyar mutum uku, kafin ’yan takara biyu su ba da sanarwar janye takararsu. Kuma sun bayyana cewa sun janye takarar ce domin su ba Kwamared Bala Halilu damar komawa shugabancin kungiyar karo na biyu.
’Yan takarar da suka bar wa Bala Halilu su ne Kwamared Babangida Garba Gwandu da Kwamared Adamu Babayo Suru, sannan sun yi kira ga magoya bayansu su yi hakuri su amince da Kwamared Bala Halilu a matsayin shugaban kungiyar ba tare da hamayya ba, su kuma ci gaba da ba shi goyon baya domin kungiyar ’yan fanshon ta ci gaba da kuma samun hadin kai.
Kuma an gudanar da zaben sauran mukamai na shugabancin kungiyar kamar Mataimakin Shugaba da Ma’ajin da Mai binciken Kudi. Sauran sun hada da Shugabar Mata da Magatakadar Mata da sauransu.
Kwamared Bala Halilu ne shugaban da ya lashe ba hamayya, sai Umar Hassan Kamba Mataimakin Shugaba, sai Umar Buda Gwadangaji Ma’aji, sai Balarabe Koko Mai bincike da Shehu Ibrahim a matsayin Amintace na daya, sai Bawa Malam Waje a matsayin Amintace na biyu. Sauran sun hada da Kulu Isah a matsayin Shugabar Mata da Hajiya Ladi Ibrahim a matsayin Magatakardar Mata.
Da yake gabatar da jawabin godiya Kwamared Bala Halilu ya bayyana jin dadinsa kan irin goyon bayan da mambobin kungiyar suka ba shi na sake zabensa karo na biyu. Ya kuma tabbatar wa mambobin kungiyar cewa, “Insha Allah zan tabbatar da na bi hakkokinku wajen gwamnati da kuma samar da ci gaba mai amfani ga kungiyar ’yan fansho ta Jihar Kebbi da kuma kare martabar mambobin kungiyar.”